An ce sinadaran dake jikin sabon nau'in gidan sauron na iya samar da karin kariyar kaso 12 bisa dari daga cutar Malaria ga wadanda suka yi amfani da shi, idan an kwatanta da gidan sauro na yanzu.
Da yake karin haske game da hakan, Farfesa Steve Lindsay, na sashen nazarin kananan halittu a jami'ar Durham, ya ce binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa, akwai ci gaba a yunkurin da ake yi na yaki da cutar malaria a yankunan kudu da hamadar Sahara, musamman ganin irin kalubalen da ake fuskanta game da yaki da cutar, bisa yadda sauro dake yada cutar ke bijirewa sinadaran da a baya ake amfani da su a gidan sauron.