Ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama, ya bayyana jajen ne a jiya, lokacin da Jakadan Indonesia a Nijeriya Harry Purwanto ya kai masa ziyara a Abuja, babban birnin kasar.
A cewarsa, suna mika jajajensu ga al'umma da Gwamnatin Indonesia a wannan lokaci da suke cikin mawuyancin hali, kuma suna musu fatan samun juriya da hakuri.
Kawo yanzu, girgizar kasar mai karfin maki 7.0 ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 105 da jikkata wasu 236, yayin da hukumomi a kasar suka kwashe masu yawon bude ido 4,600 daga tsibirai 3 dake kusa da Lambok. (Fa'iza Mustapha)