in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda ake mai da hamada dausayi, rairayi ya zama zinari a hamadar Kubuqi
2018-08-08 10:13:33 cri

Hamadar Kubuqi dake jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta a kasar Sin, Hamada ce mafi girma ta 7 a kasar, wadda fadinta ta kai kilomita 365 daga gabas zuwa yamma, kuma kimanin 40 daga kudu zuwa arewa. Kana wani bangare ne na birnin Ordos na jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta da ke arewacin kasar Sin. Kwanan nan, wakiliyarmu Faeza Mustapha ta samu damar zuwa yankin, inda ta shafe tsawon kwanaki bakwai. Yanzu a saurari wani rahoton da ta hada mana dangane da ziyarar.

Kwararar Hamada babbar matsala ce da al'ummomin duniya suka daura damarar yaki da ita domin kyautata muhallin rayuwar bil'adama, kuma gaskiya hamadar ta Kubuqi ta zama misali, saboda nasarorin a zo a gani da aka cimma a kokarin da aka yi na daidaita ta, ganin cewa a cikin shekaru kimanin 30 da suka wuce, an daidaita sassan hamadar da fadinsu ya kai sama da muraba'in kilomita 6000, wato kimanin kashi daya daga cikin uku na fadin hamadar ta Kubuqi baki daya. An mai da hamada dausayi ke nan. Sai dai abin da ya fi ba ni sha'awa a wannan ziyarata a hamadar Kubuqi shi ne, yadda aka mai da aikin yaki da hamada hanyar samun arziki, wato baya ga kyautata muhallin rayuwar mazauna wurin.

Liquorice nau'in maganin gargajiya ne da ake yawan amfani da shi a kasar Sin. Baya ga haka, wani nau'in tsiro ne da kan rayu a sassan da ke fama da karancin ruwa, wanda kuma ke iya gyara hamada da kara mata sinadarai don zama kasa mai inganci. A hamadar Kubuqi, akwai wani kamfani mai suna Elion da ya fara shuka nau'in tsiro na Liquorice daga karshen shekarun 1990. Kuma abin da ya fi jawo hankalina shi irin tsarin da ake bi wajen noman Liquorice. tsarin da nake ganin na hadin gwiwa ne da samun moriyar juna. A kauyen Hangjin Naoer da na ziyarta, kamfanin Elion ya hada gwiwa da manoman kauyen, yana samar da irin Liquorice da fasahar noma ga manoma, kuma manoma ne ke ba da hayar filayensu na hamada ga kamfanin don su shuka irin da aka ba su tare kuma da kula da su. Baya ga haka, da tsiron ya girma bayan shekaru uku, kamfanin Elion zai saye su daga hannun manoma, inda zai harhada magunguna iri iri ya sayar kuma ya ci riba, kana manoma ma su kara samun kudin shiga bisa ga sayar da tsiron, kuma kudin da suke samu daga noman tsiron ya ninka wa masara da suka saba nomawa har sau bakwai zuwa takwas. Muna iya gano cewa, wannan tsari yana tattare da alfanu ta fannoni da dama: Na farko, noman Liquorice ya taimaka ga kyautata muhalli da kuma gyara hamada. Na biyu, kamfanin ya ci riba daga harhada maganin. Na uku, manoma mazauna hamada da suke cikin kangin talauci sun samu kudin shiga bisa ga noman tsirran.

Kullum sake kara ilimi da haduwa da sabbin abubuwa nake a ziyarata a Hamadar Kubuqi, ko da yake, an ce tafiya mabudin ilimi ce. A ziyarata a yankin hamadar Kubuqi, na kuma samu damar ganin gonaki a tsakiyar Hamada, kuma abun mamaki shi ne, baya ga wadanda aka yi a filin, akwai kuma wadanda aka yi a cikin rumfa, inda aka shuka kayan lambu daban-daban. Kamar yadda na bayyana a baya, noman Liquorice a hamada zai iya taimakawa ga gyara hamada, kuma a hamadar da aka daidaita, za a iya sauran shuke-shuken da suka hada da Tumatir da Cucumber da nau'ika daban-daban na kankana da kayakin lambu.

Malam Sun Yongqiang, wanda yake kula da gonar, ya bayyana mini wasu matakai uku da ake bi wajen kafa gonaki a cikin hamada, na farko, kafa shingayen kare kwararar hamada. Na biyu kuma, farawa da noman Liquorice don daidaita hamada. Na uku, bayan kimanin tsawon shekaru uku na noman Liquorice, za a iya fara noman sauran kayakin lambu a kan kasar da ta inganta.

Daya daga cikin abubuwan da ba a raba Hamada da shi, shi ne hasken rana. A Hamadar Kubuqi na ga yadda aka yi amfani da wannan albarka wajen kyautata muhalli da rayuwa, har ma da samun kudin shiga. Wato Kamfanin Elion, ya yi amfani da hasken ranar dake akwai wajen samar da wutar lantarki. Ya kafa daruruwan farantai ko solar panels dake samar da wuta daga hasken rana, inda suke samar da wutar lantarki mai karfin KWH milyan 500 a kowacce shekara, wanda ke samar da wuta ga yankin yammacin jihar Mongoliya ta gida, wanda ke dauke da gidaje da masana'atu.

Abun ban sha'awa shi ne, an kafa wadancan Farantai ne ta yadda za su kare kwararar Hamada, sannan a iya shuke-shuke da kiwon kaji da agwagi daga karkashinsu. Wadannan farantan da aka kafa, baya ga samar da wutar lantarki, sun kuma taimaka ga kare tsirran da aka shuka daga iska da rairayi, a yayin da tsirran da aka shuka za su taimaka ga rike kasa da kuma gyara hamada. Har wa yau, najasar dabbobin da ake kiwo ma za ta taimaka ga inganta kasa. Wannan yunkuri ya kuma ba mutanen yankin damar samun aikin yi da kyautata rayuwarsu, domin kuwa manoma mazauna wurin ne suka ba kamfanin hayar filayensu na hamada don ya gyara ya kafa farantansa na samar da wuta, shi kuma kamfanin ya ba manoma damar shuke-shuke da kiwon dabbobi daga karkashin farantan, kuma shi ne yake taimakawa ga sayar da kwai da naman dabbobin da manoman ke kiwo zuwa kasuwanni. Har wa yau, kamfanin yana ba manoman damar aikin tsaftace farantan, kuma yana biyan su ladan aikin. Wang Sitang, wani manomi a yankin da na zanta da shi, ya shaida min cewa, a baya kudin shigar da kowane iyali ke samu ba ya wuce yuan dubu 10 a shekara, amma yanzu bisa noma da aikin kula da wadancan farantai da suke yi, kowane iyali na samun kudin shigar da ya kai yuan dubu 50 zuwa dubu 60 a kowacce shekara.

Zan iya cewa yabon gwani ya zama dole. Domin namijin kokarin da aka yi a Hamadar Kubuqi, ya cancanci yabo matuka, sannan darasi ne da ya kamata al'ummomi duniya su dauka. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China