in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fasahar yaki da hamadar Kubuqi da kasar Sin ta samu za ta iya amfana wa kasashen Afirka wajen yakar hamadar Sahara
2018-08-09 15:14:54 cri

Hamadar Kubuqi dake jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta a kasar Sin, Hamada ce mafi girma ta 7 a kasar, wadda fadinta ta kai kilomita 365 daga gabas zuwa yamma, kuma kimanin kilomita 40 daga kudu zuwa arewa. Kana wani bangare ne na birnin Ordos na jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta da ke arewacin kasar Sin.

A 'yan kwanakin baya baya nan, wakilinmu Faeza Mustapha ta yi tattaki har zuwa yankin wannan Hamada, inda ta shafe kwanaki bakwai. Kwararar Hamada babbar matsala ce da al'ummomin duniya suka daura damarar yaki da ita domin kyautata muhallin rayuwar bil'adama, kuma gaskiya hamadar ta Kubuqi ta zama misali, saboda nasarorin a zo a gani da aka cimma a kokarin da aka yi na daidaita ta, ganin cewa a cikin shekaru kimanin 30 da suka wuce, an daidaita sassan hamadar da fadinsu ya kai sama da muraba'in kilomita 6000, wato kimanin kashi daya daga cikin uku na fadin hamadar ta Kubuqi baki daya. An mai da hamada dausayi ke nan. Sai dai abin da ya fi ba ni sha'awa a wannan ziyarata a hamadar Kubuqi shi ne, yadda aka mai da aikin yaki da hamada hanyar samun arziki, wato baya ga kyautata muhallin rayuwar mazauna wurin. A cikin shirinmu nay au, a ganin malama Faeza Mustapha, fasahohin yaki da hamadar Kubuqi da kasar Sin ta samu za su iya amfanawa kasashen Afirka wajen yakar hamadar Sahara. (Faeza Mustapha, Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China