in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
INEC Ta Nemi A Hada Karfi Domin Hana Sayen Kuri'u
2018-08-01 16:36:45 cri
A labarin da jaridar "Leadership" Najeriya ta bayar, an ce, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasar INEC, ta yi kira da babbar murya ga dukkan wadanda ke da alhakin sa baki, a goya wa hukumar baya wajen hada karfi domin a kawar da mummunar illar sayen kuri'u a lokutan zabe masu zuwa.

Ba a kan laifukan sayen kuri'u INEC ta tsaya da yin kiran ta ba, hukumar ta hada har da sauran dukkan laifukan da suka ribinci zabe.

Shugabar Bangaren Bada Shawarwari Kan Batutuwan Shari'a ta hukumar, mai suna May Agbamuche-Mbu ce ta yi wannan kira ne a lokacin da ta ke jawabi wurin taron kwanaki biyu da aka gudanar a Lagos.

An gudanar da taron ne na sanin makamar aiki ga jami'an 'yan sanda, domin kara dora su kan turbar yadda ake gabatar wa kotu wadanda aka kama da aikata laifukan da suka danganci karya dokokin zabe.

INEC ce da kan ta ta shirya wannan taro tare da hadin gwiwar Cibiyar Taimakawa Kan Zabubbuka Ta Tarayyar Turai.

Agbumuche-Mbu ta kara da cewa sayen kuri'u da sauran laifukan karya dokokin zabe, su na rage wa zabuka inganci da sahihanci. Wannan kuwa inji ta, ya na shafar hatta ita kan ta dimokradiyyar ya na rage mata karsashi sosai.

Ta ci gaba da cewa, duk da ya ke INEC na da iyaka ko karancin kayan aiki, da ma'aikatan da za su hana wannan harkalla, hukumar za ta ci gaba da yin iyakar kokarin ta, wajen ganin an magance wannan babbar matsala.

Daga nan sai ta yi kira ga jami'an tsaro, 'yan siyasa, kungiyoyin sa-kai da sauran jama'a da su taya INEC wannan babban aiki na kawo karshen sayen kuri'u a lokutan zabe, da ma sauran laifukan da suka shafi karya dokokin zabe a Najeriya.

Ta ce abun da ya faru dangane da yawaitar saye da sayar da kuri'u a zaben gwamnan jihar Ekiti, ya zama ishara da zai sa kowa ya nuna damuwa, kuma a tashi tsaye gaba daya domin a kawar da wannan mummunar dabi'a.

Ta ce an shirya wa 'yan sanda wannan taro na sanin makamar aiki ne, domin sau da yawa ana bar wa INEC nauyin gurfanar da masu laifin zabuka a gaban kotu, wanda aikin masu gabatar da kara ne.

Ta karkare da cewa, dalili ma kenan INEC ta yi kira tuni aka kafa Hukumar Ladaftar da Masu Aikata Laifukan Zabe ta Kasa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China