in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmancin BRICS ga kasashe masu tasowa
2018-08-02 09:06:08 cri

Daga ranar 25 zuwa 27 ga watan Yulin wannan shekara ce aka gudanar da taron kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa (BRICS) wato, Brazil, Rasha, Indiya, Sin da kuma Afirka ta kudu, karo na 10 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu .

Wannan shi ne karo na biyu da ake gudanar da taron na BRICS a kasar Afirka ta kudu, bayan wanda ya gudana a shekarar 2013. Taken taron na bana shi ne "BRICS a Afirka"

Kungiyar ta samo asali ne a shekarar 2001, lokacin da Jim O'Neill, babban masani kan tattalin arziki dake aiki a kamfanin Goldmansachs na Amurka ya fara tunanin wannan ra'ayi na "Kasashen BRIC" a karo na farko a duniya.

A watan Yuni na shekarar 2009, shugabannin kasashen BRIC suka yi ganawar farko a hukunce a kasar Rasha. Daga bisani, a watan Disamba na shekarar 2010, kasashen na BRIC suka cimma matsaya daya wajen shigar da kasar Afirka ta Kudu cikin kungiyar, haka ya sa BRIC ya zama BRICS.

Daga bisani shugabannin kungiyar kasashen (BRICS) yayin taron kungiyar karo na 6 a Fortaleza na Brazil sun bayyana aniyyarsu ta kafa wani bankin musamman na tsimi da samar da ci gaba.

Manufar kungiyar ta BRICS ta kafa bankin, wanda ya fara aiki da jarin dalar Amurka miliyan dubu 100, ita ce baiwa kasashe mabukata, musamman masu tasowa damar kaucewa fadawa matsalolin kudi da samar da rance domin rage kaifin matsalolin tattalin arziki. Har wa yau ana fatan wannan tsari zai taimaka wajen kara hada kan kasashe mambobin kungiyar tare da baiwa tsarin tattalin azikin duniya kariya ta musamman bisa tsare-tsaren da ake da su a halin yanzu.

Kana yayin taron kungiyar karo na 9 da ya gudana a Xiamen na kasar Sin, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya bayyana kudurin kasarsa na samar da dala miliyan 500 ga bankin a matsayin kudin ajiya. Ya kuma bayyana cewa, baki daya shugabannin kasashen BRICS suna ganin cewa, zurfafa hadin gwiwa a fannin harkokin siyasa da tsaro, da kara amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare sun dace da muradun kasashen biyar kamar yadda sauran kasashen duniya ke fatan gani.

Ya ce, suna goyon bayan ci gaba da sa kaimi ga ci gaban hadin gwiwa a fannin siyasa da tsaro, don taka rawar da ta dace, a fannin kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya.

Masana na ganin cewa, wannan manufa ta BRICS, za ta taimaka wajen daga matsayin kasashen kungiyar na yada manufofi da tunaninsu a harkokin duniya, baiwa kasashe masu tasowa ikon fadin albarkacin baki da kuma shimfida yanayi mai kyau ga tattalin arzikin duniya. (Saminu, Ahmed, Ibrahim /Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China