Yayin da wannan ziyarata mai kunshe da dimbin ilimi da nishadi da tarihi ke kammala, na samu damar ganin hanya ta farko da ta ratsa Hamada a kasar Sin. Gwamnati ta fara ginin hanyar mai tsawon kilomita 115 ne a shekarar 1997, ta kuma kammala a shekarar 1999. Kafin ginin hanyar, manoma da makiyaya mazauna hamadar Kubuqi sun fuskanci wahalar shigar da kayayyakin rayuwarsu na yau da kullum da kuma fitar da kayaykinsu na sayarwa. Amma bayan kammala ginin titin, al'ummar wannan yankin sun samu sauki sosai, domin ta kyautata rayuwarsu ta hanyar bunkasa musu kudin shiga da tattalin arziki da saukaka sufurin, aikin da a baya suke ganin tamkar ba za a taba iyawa ba. Menkenbayaer, mazaunin yankin mai shekaru 48 da haihuwa, ya ce su makiyaya, sun yi matukar farin ciki da kaddamar da wannan hanya, a cewarsa, "A da a kan kwashe kwana daya wajen dauko abinci daga cikin gari, amma bayan kaddamar da wannan hanya, sa'a daya kadai ake dauka."(Faeza Mustapha)