in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CBN ta bukaci jama'a su guji wulakanta takardar naira
2018-07-30 10:38:01 cri
Babban bankin kasa (CBN) ta nuna rashin jin dadin shi a kan yadda ake yi wa takardun kudi, yadda ake lankwasa su da sayar da su da zuba su da kuma hawa kansu lokacin da ake yin rawa. Dama yarda wasu ke boye su. Gwamnan Babban bankin kasa Mr Godwin Emefiele ya ja kunnen mutane cewar, daga yanzu, duk wadanda aka kama suna karya wannan dokar , za a daure zuwa wata shida gidan Fursuna, ko kuma tarar Naira 50,000, ko ma a hada duka. Kamar dai yadda dokar Babban Bankin ta shekarar 2007 ta bayyana da kuma tanada. Ya ce, ya kamata su kudaden kasa a ba su darajar da ta dace da su, kamar dai yadda za a ba tuttar kasa daraja, Babban bankin Nijeriya tana kashe fiye da Naira 100 saboda kawai ta buga Naira 100. Emefiele ya yi wannan bayanin ne a lokacin da aka yi taron kwana biyu a kan fadakarwa da kuma wayar da kan jama'a, mai taken ''Yadda za a samar daidaituwar harkar kudade da kuma bunkasa tattalin arziki'' wanda aka shiryawa masu masana'antu, masu yin kayayyaki, masu kitso, masu gidan biredi, da kuma mambobin hadaddiyar kungiyar manoma, teloli, makanikai, da dai sauransu, wanda aka bude a Owerri ranar Juma'a.

Babban bankin kasa ranar Jumma'a ne ya fara kawo dauki ia karkashin tsarin yarjejeniyar yadda za a saukaka harkar kasuwanci, inda ya sa kudin kasar China wato Sin CN milyan 69.85 a kasuwar hada hadar kasuwanci ta kasashen waje. Mai rikon mukamin darektan sadarwa na Babbab bankin CBN Isaac Okorafor, shi ya bayyana tabbacin hakan. Ya kara da bayanin cewar baya ga su kudaden China da aka sa, har ila yau shi Babban bankin ya sa dalar Amurka milyan 340.5 a harka ta tsakanin bankuna. (Leadership a Yau)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China