in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Turai ba ta sha'awar sayen waken soya na Amurka
2018-07-29 17:58:27 cri

Kwanan baya, shugaban Amurka Donald Trump ya yi shawarwari tare da shugaban kungiyar tarayyar Turai ko kuma EU a takaice, Jean-Claude Juncker, inda ya sanar da cewa, Amurka da EU sun amince ba zasu kara sanyawa juna kudin fito kan hajojinsu ba yayin da suke ci gaba da yin shawarwari, al'amarin da ya sassauta takaddamar cinikayyar dake tsakaninsu.

A wadannan kwanaki, game da wasu manufofi uku da Donald Trump ya bullo da su, ciki har da daina sanyawa juna harajin kudin fito, da cire duk wani shinge game da sauran wasu matakai na ba da kariya ga cinikayya, gami da daina samar da kudin rangwame ga kayayyakin da ba su shafi motoci ba, bangarorin biyu wato Amurka da EU sun yi bayanai mabambantan.

A wani gangamin siyasa da aka yi a ranar 26 ga wata a jihar Iowa mai dogaro da aikin gona, Trump ya bayyanawa taron gangamin cewa, gwamnatinsa ta bude kofar kasashen Turai ga manoman Amurka, ta yadda za su samu babbar kasuwa a Turai.

Amma a nasu bangaren, jami'an kungiyar tarayyar Turai sun ce, aikin gona ba wani bangare ba ne a cikin shawarwarin EU da Amurka, sai dai kawai bayanan da aka tabbatar da su a cikin sanarwar da suka fitar tare.

Shi ma shugaban Faransa gami da firaministan Spaniya sun maida martaninsu game da furucin Trump, inda Emmanuel Macron na Faransa ya ce, ya ki amincewa da a sanya batun aikin gona cikin kowace irin yarjejeniyar kasuwanci, inda ya ce a ganinsa, a fannonin da suka shafi muhalli da lafiya gami da abinci, bai kamata a saukar da duk wani ma'aunin Turai ba. Sa'annan firaministan kasar Spaniya ya ce ya kamata a kare manufofin bai daya na EU.

Koda yake wasu shugabannin kasashe mambobin kungiyar EU sun ki amincewa da shigar da batun aikin gona cikin shawarwari kan yarjejeniyar cinikayya da Trump ya gabatar, amma kungiyar EU ta yi alkawarin ci gaba sa kaimi a wannan fanni.

Amma shin ko kungiyar EU na da karfin taimakawa Amurka wajen warware matsalar waken soya?

Kamfanin dillancin labarai na Amurka na Bloomberg ya ce wannan ba zai yiwu ba, inda ya ce, kasuwar Turai na daya daga cikin kasuwanni kalilan dake iya maye gurbin kasuwar Sin wajen sayen waken soya na Amurka. Amma karfin sayayyarta bai kai na kasar Sin ba. Jimillar cinikayya ta sayen waken soya daga Amurka da kasar Sin ta yi a bara ya kai Dala biliyan 12.3, amma wannan jimilla ta kai Dala biliyan 1.6 kawai ga kungiyar EU. Haka zakila an yi hasashen cewa, yawan waken soya na Amurka da kasashen Turai za su bukata zai kai ton miliyan 15.3 a tsakanin shekarar 2018 da ta 2019, jimillar bai kai kashi daya cikin kashi shida bisa yawan bukatun da kasar Sin ta tsara ba a da. Gwamnatin Trump ta tada takaddamar cinikayya da kasar Sin, wadda ta samu martani mai tsanani daga wajen kasar Sin. Lamarin da ya kawowa manoman Amurka asarar waken soya, kana ya kara matsin lamba a siyasance ga Trump da 'yan jam'iyyar Republican na jihohi masu dogaro da aikin gona. Lallai wadannan matsaloli ba Turai ke iya warware su ba.(Murtala Zhang, Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China