in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya kammala ziyararsa ta farko a bana
2018-07-29 17:09:28 cri

Bisa gayyatar da shugaban masarautar hadaddiyar Daular Larabawa, da shugaban jamhuriyar kasar Senegal, da shugaban jamhuriyar kasar Ruwanda, da shugaban jamhuriyar kasar Afirka ta Kudu suka yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gudanar da ziyarar aiki a wadannan kasashe hudu, tsakanin ranekun 19 zuwa 24 ga wannan wata na Yuli. Kana bisa gayyatar da shugaban Afirka ta Kudu ya yi masa, shugaba Xi ya halarci taron ganawa tsakanin kasashen mambobin BRICS karo na 10, wanda aka shirya a Johannesburg, tsakanin ranekun 25 zuwa 27 ga watan Yulin da muke ciki. Bayan kammala dukannin ayyukan, shugaba Xi ya yada zango a kasar Mauritius, inda ya gudanar da ziyarar sada zumunta. Ziyarar da shugaba Xi ya yi, ziyararsa ta farko ce a kasashen ketare a shekarar bana da muke ciki, bayan kammalar ziyarar, mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya gayawa manema labarai cewa, ziyarar tana da ma'anar tarihi, musamman ma wajen raya hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashe masu tasowa da kuma kasashen da suka fi saurin ci gaban tattalin arziki.

A ziyarar ta tsawon kwanaki 11, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara a birane 6 dake kasashe 5, tsayin ziyararsa ya kai kilomita dubu 36, kana adadin ayyukan da aka shirya tsakanin bangarori biyu ko bangarori da dama da shugaba Xi ya halarci yayin ziyarar ya zarta 60, haka kuma gwamnatocin wadannan kasashen biyar sun shirya gaggaruman bukukuwa domin maraba da zuwansa kasashensu, ziyarar ta yi matukar jawo hankalin kafofin watsa labarai na kasar Sin da kasashen waje baki daya.

Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana cewa, ziyarar Xi a wannan karo ta bude wani sabon shafi ga ci gaban huldar diplomasiya dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya, haka kuma ta daga matsayin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa zuwa wani sabon matsayi, har ta ingiza aikin gina kyakkyawar makoma ga duk bil Adama gaba yadda ya kamata.

Har kullum, shugaba Xi yana maida hankali sosai kan huldar dake tsakanin kasarsa da kasashen Afirka, a shekarar 2013, wato tun farkon da ya hau kan kujerar shugaban kasar Sin, da kuma bana, lokacin da ya sake rike wannan mukamin, sau biyu ne ya zabi nahiyar Afirka da ta zama wurin da ya yi ziyararsa ta farko.

Wang Yi ya bayyana cewa, yayin ziyarar, gaba daya shugaba Xi da sauran shugabannin kasashen Afirka hudu sun cimma matsaya guda kan batun game da kara zurfafa fahimtar juna a fannin siyasa dake tsakaninsu, da sanya kokari tare domin neman samun wata hanyar raya kasa mai dacewa, tare kuma da nuna goyon baya ga juna a cikin harkokin kasa da kasa, da kuma harkokin shiyya shiyya.

Shugabannin kasashen Afirka sun bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka zai samar da damammaki gare su domin samun moriyar juna, ko shakka babu kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasashen Afirka, bai kamata ba a zargeta cewa wai tana gudanar da sabon mulkin mallaka a nahiyar Afirka. Kasashen Afirka sun lura cewa, kasar Sin sahihiyar aminiyarsu ce, a don haka suna son sanya kokari tare da kasar Sin domin cimma burin Afirka da burin kasar Sin.

Yayin ziyarar, shugaba Xi ya daddale yarjejeniyoyin fahimtar juna da kasashen Senegal da Ruwanda bisa shawarar ziri daya da hanya daya, bayan da ya kulla irin wannan yarjejeniya da kasar ta Afirka ta Kudu, haka kuma ya cimma matsaya guda da kasar Mauritius kan batun kulla jarjejeniyar dake shafar shawarar ziri daya da hanya daya, duk wadannan sun samar da wani sabon dandalin hadin gwiwa ga sassan biyu wato Sin da Afirka. Gaba daya adadin yarjejeniyoyin da aka daddale yayin ziyarar ya kai kusan 40, ana sa ran cewa, kokarin da suke zai amfanawa al'ummomin sassan biyu baki daya.

Wang Yi ya kara cewa, bana shekara ce mai muhimmanci yayin da ake raya huldar dake tsakanin Sin da Afirka, a watan Satumba dake tafe, za a gudanar da taron kolin dandalin taron hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a nan birnin Beijing, ya zuwa wancan lokaci, za a yi nazari kan shawarar ziri daya da hanya daya da ajandar samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 ta MDD da ajandar raya kasashen Afirka nan da shekarar 2063 ta AU, tare kuma da tsare-tsaren raya kasa na kasashen Afirka, domin samar da wani sabon tsarin gudanar da hadin gwiwa daga duk fannoni dake tsakanin Sin da Afirka.

Kana kasashen mambobin kungiyar BRICS suna samun ci gaba yadda ya kamata a cikin shekarun baya bayan nan, shi yasa shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata su kara kyautata huldar abokantaka dake tsakaninsu domin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin duniya, tare kuma da zurfafa cudanyar al'adu dake tsakaninsu.

Yayin ziyararsa, shugaba Xi ya yi kira da a kafa tsarin tattalin arizkin duniya ba tare da rufa rufa ba, haka kuma a kara zurfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa bisa tsarin yin hakuri ga bambancin ra'ayi.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China