Yau na ga yadda aka yi kokarin samar da ruwa a cikin Hamada, ta samar da ruwa daga rawayan kogi da ba shi da nisa daga yankin Hamada. An samar da hanyar da ruwa za ta rika fita daga kogin zuwa yankin Hamada. Wannan yunkurin yaki da Hamada sannan kuma na magance ambaliyar a lokacin da kogin ya tumbatsa.
Daga nan kuma mun je mun ga irin matsugunin makiyaya na da kafin Gwamnati ta samar masu da mutsugunai na zamani, inda na yi ciye ciye sosai kamar na kindirmo da cukwi da cincin da wasu abubuwan da dama da aka sarrafa su da madarar shanu.(Faeza Mustapha)