in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kolin shugabannin kasashen BRICS karo na 10
2018-07-27 13:49:29 cri

Jiya Alhamis ne a birnin Johannesburg na Afrika ta kudu, aka bude taron kolin shugabannin kasashen BRICS karo na 10. Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa shi ne ya jagoranci taron, wanda ya samu halartar shugaban Sin Xi Jinping, na Brazil Michel Temer, na Rasha Vladimir Putin, da firaministan kasar Indiya Narendra Modi. Yayin ganawar, shugaba Xi ya nuna cewa, ya kamata kasashen BRICS su yi amfani da wannan zarafi mai kyau don zurfafa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, da inganta hadin kai ta fuskoki uku wato tattalin arziki, siyasa da al'adu, ta yadda za a kai ga bude wani sabon babi na hadin kai a tsakaninsu a cikin shekaru 10 masu zuwa.

A yayin ganawar da aka yi a wannan rana, bangarorin sun yi musanyar ra'ayi kan yadda kasashen BRICS za su hada kai bisa taken "BRICS a Afrika: Samun bunkasuwa mai wadata tsakanin bangarori da dama cikin hadin kai a yayin juyin juya halin masana'antu karo na hudu". Bangarorin daban-daban sun kuma sun ba da sanarwar shugabannin BRICS na Johannesburg, inda suka isar da sakon kiyaye kasancewar bangarori daban-daban a duniya da yaki da manufar ba da kariyar cinikiyayya. Sun kuma kai ga cimma matsaya game da raya dangantakar abota kan sabon kwaskwarimar masana'antu, da kara hadin kai a fannoni ciniki, tattalin arziki, hada-hadar kudi, tsaro, siyasa, yin musanyar al'umma da sauransu. A nasa jawabin, Mista Xi ya ba da shawara kan yadda kasashen BRICS za su kara hada kansu nan gaba da nanata wajibcin raya duniya mai wadata tsakanin bangarori daban-daban.

Mista Xi ya bayyana cewa, ya kamata BRICS su yi amfani da zarafi mai kyau a halin yanzu, don tabbatar da bude sabon babi a cikin shekaru 10 masu zuwa. Ya kuma nuna cewa, kara hadin kai ta fuskar tattalin arziki da samun bunkasuwa tare shi ne babban tushen da mambobin suka yi amanna a kai, ganin yadda kasashen suka samu ci gaba mai armashi, ya kamata bangarori daban-daban su kara sa kaimi ga hadin kansu, ya ce:

"Ya kamata, mu kara hada kai ta fuskar zuba jari, hada-hadar kudi da kara tuntubar juna a dukkanin fannoni da dai sauransu. Tare kuma da kiyaye tsarin yin ciniki tsakanin bangarori daban-daban, da sa kaimi ga yin ciniki da zuba jari ckin 'yanci da yaki da manufar ba da kariya bisa tsarin MDD, G20 da WTO da sauransu. Kamata ya yi mu nace ga hada tsare-tsarenmu na samun bunkasuwa tare ta hanyar yin amfani da karfin kirkire-kirkire da kafa sabon dangantakar abota na kwaskwarimar masana'antu, da kuma kara sulhuntawa ta fuskar daidaita harkoki daga manyan fannoni."

Xi Jinping ya bayyana cewa, Sin za ta aiwatar da aikin inganta rayuwar dam Adam guda 10 idan yake fatan gayyatar kwararrun kasashen biyar kan yadda za su tsara taswirar sabon kwaskwarimar masa'anatu tare, ta yadda za a kara karfin takara na kasashen BRICS da ma kasashe maso tasowa.

Game da hadin kansu a fannin tsaron siyasa, Mista Xi ya ce:

"Dole ne mu ci gaba da martaba ra'ayin kasancewar bangarori daban-daban a duniya, da kiyaye tsari da ka'idar MDD, tare kuma da kalubalantar bangarori daban-daban da su rika martaba dokokin kasa da kasa da manyan ka'idojin dangantakar kasa da kasa, don daidaita bambamcin ra'ayi da korafe-korafe ta hanyar yin shawarwari. Kamata ya yi, mu bayyana ra'ayoyinmu da gabatar da shirye-shiryenmu ta yin amfani da wasu manyan tsare-tsare don kafa wata sabuwar dangantakar kasa da kasa ta mutunta juna, samar da daidaici da adalci da samun moriyar tare cikin hadin kai, ciki hadda ganawar ministocin kasa da kasa, ganawar wakilan dindindin na MDD da dai sauransu."

Hakazalika, Mista Xi Jinping ya ce, kasashen BRICS suna da al'adu mai dogon tarihi, akwai babbar yiwuwar hadin kai ta fuskar tutunbar zaman takewar al'umma a tskaninsu. Ya ce:

"Ya kamata mu ci gaba da tuntubar juna a fannoni al'adu, ba da ilmi, kiwon lafiya, yawon shakatawa da sauransu bisa ka'idar hada zukatun jama'a tare. Sin na ba da shawarar kafa dakin nune-nune na BRICS, dakin nuna zane-zane, bikin nuna litattafai da sauransu, da kuma kara hadin kai ta fuskar sana'ar kirkire-kirkire, yawon shakatawa, birane daban-daban da sauransu. Ta yadda za a bayyana labarai dake suka shafi kasashen BRICS masu burgi da kara fahimta tsakanin al'ummomin kasashen BRICS da zurfafa dankon zumunci tsakaninsu."

Ban da wannan kuma, Mista Xi ya nuna cewa, tun kafuwar tsarin BRICS da farko, bangarori daban-daban na tabbatar da ka'idar samun bunkasuwa tsakanin bangarori da dama, kuma an tabbatar da tunanin BRICS+, wato samun bunkasuwa tare na bude kofa tsakanin kasashe masu tasowa, don tabbatar da muradun wadannan kasashe da kara ba da gudunmawarsu wajen tabbatar da zaman lafiyar duniya.

Shugabanni mahalartan taro sun bayyana cewa, ya kamata kasashen BRICS su kara hada kansu a halin yauzu da yada tunanin kasancewar bangarori daban-daban da kokarin yin ciniki cikin 'yanci. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China