in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarata a Kubuqi 5
2018-07-26 20:28:37 cri

Baya ga kokarin kyautata rayuwar masu karamin karfi yayin da ake yaki da Hamada a Hamadar Kubuqi, ba a manta da ilimi ba. An ce ilimi gishirin rayuwa, kuma matasa masu ilimi, su ne karfin kowace al'umma. Yau na kai wata makaranta mai suna

Elion Oriental School, makarantar da ta kunshe gidan reno da firamare da kuma midil, kuma wani abu da ya jawo hankalina shi ne cikin darrusan da ake koyarwa, har da na kiyaye muhalli, inda tun yanzu ake koyawa daliban hanyoyi daban-daban na kiyaye muhalli, domin su tashi da ilimin da kuma burin kyautata muhalinsu. Yayin zantawata da Du Yushu, mai shekaru 15, wadda a yanzu ke karatun midil a makarantar, ta ce akan shirya wasanni domin fadakar da su ilimin kiyaye muhalli, sannan su kan je Hamada tare da abokan karatunta domin dasa bishiyoyi.(Faeza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China