in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya halarci taron masu masana'antu da 'yan kasuwa na kasashen BRICS
2018-07-26 13:20:25 cri

Jiya Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron dandalin tattaunawar harkokin masana'antu da kasuwanci na kasashen BRICS da aka yi a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu. A jawabinsa Shugaba Xi ya ce, duniya na fuskantar manyan canje-canje a halin yanzu, kuma wannan wata kyakkyawar dama da kuma kalubale ne ga kasashe masu tasowa da ma kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa. Ya kamata mu karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS bisa halin da muke ciki, da dukufa wajen raya kasashenmu a lokacin da kasashen duniya ke kokarin bunkasa da kuma ci gaban kasashen BRICS, ta yadda za a kai ga sabon matsayi na samun bunkasuwa cikin shekaru goma masu zuwa.

Yanzu ga karin bayani da Maryam Yang ta hada mana:

Cikin jawabinsa mai taken "neman ci gaba cikin hadin gwiwa, bisa halin da muke ciki", shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, shekaru 10 masu zuwa, za su kasance lokaci na musamman na sauya tsohon tsarin tattalin arzikin duniya zuwa sabon tsari, da lokaci na samun sauyin yanayin siyasar kasa da kasa, da gyara tsarin gudanarwar harkokin kasa da kasa daga tushe. A wannan lokaci na musamman, ya kamata kasashen BRICS su kara zakulo damammakin neman bunkasuwa, warware matsalolin dake gabanmu cikin hadin gwiwa, domin ba da gudummawa yadda ya kamata wajen gina sabuwar dangantaka a tsakanin kasashen duniya, da kuma kara samar da al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil Adama.

Haka kuma, Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata mu ci gaba da yin hadin gwiwa domin cimma moriyar juna, da bullo da tsarin tattalin arziki mai bude kofa ga waje. Ya ce,"Ya kamata mu bi hanyar yin hadin gwiwa da bude kofa ga waje, idan muna son samun bunkasuwar kimiyya da fasaha da kuma raya harkokin masana'antu. Bai dace a rika tayar da yakin ciniki a duniya ba, sabo da babu wanda zai yi nasara a yakin. Ko tsarin tattalin arziki mai tallafawa bangare daya kawai, wanda zai kawo illa ga muradun gamayyar kasa da kasa. Ya kamata kasashen BRICS su ci gaba da gina tsarin tattalin arziki mai bude kofa ga kowa, da kuma yaki da kariyar ciniki, domin inganta yanayin adalci da 'yanci cikin harkokin zuba jari da ciniki, ta yadda tattalin arzikin duniya zai samu ci gaba ta hanyar adalci, nuna fahimta da kuma cimma moriyar juna. Bugu da kari, ya kamata a taimakawa kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa da kasashe masu tasowa a yayin da muke dukufa wajen dunkulewar tattalin arzikin duniya, musamman ma ga kasashen Afirka da wasu kasashe masu fama da talauci."

Xi Jinping ya ce, ko wace kasa tana da ikon neman bunkasuwa cikin yanayin adalci, bisa sabbin damammakin da aka samu, domin bunkasuwar sabbin fasahohi. Ya kamata a ci gajiyar damammakin, kara zuba jari kan harkokin neman sabuntawa, mai da hankali kan raya sabbin harkokin da za su bunkasa tattalin arziki, ta yadda za a canja tsohon tsarinmu na raya tattalin arziki zuwa sabon tsari. Ya ce, "Ajandar neman dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 ya zayyanawa gamayyar kasa da kasa daftarin neman ci gaba. Ya kamata kasashen BRICS su hade tsarinsu na neman raya kansu da wannan jadawalin tare, wajen gudanar da ayyukan raya tattalin arziki da zaman takewar al'umma, ta yadda za su kara tallafawa al'ummominsu, don su ji dadin zaman rayuwarsu. Bugu da kari, ya kamata mu kare muhalli yadda ya kamata, sa kaimi ga gamayyar kasa da kasa su aiwatar da yarjejeniyar Paris, gaggauta bullo da tsarin neman bunkasuwar ba tare da gurbata muhalli ba. A sa'i daya kuma, akwai bukatar kasashen duniya su hada kai, wajen sa kaimi ga kasashe masu ci gaba da su goyi bayan kasashe masu tasowa kan wannan aiki, kamar yadda jarjejeniyar ta bayyana."

Xi Jinping ya kara da cewa, nahiyar Afirka nahiya ce mai kunshe da kasashe masu tasowa, kuma nahiyar da ta fi samun karfin neman bunkasuwa a duk fadin duniya. Ya kamata mu kara yin hadin gwiwa da kasashen Afirka, ba su taimako wajen neman bunkasuwa, da kuma mai da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen BRICS da kasashen Afirka a matsayin abin koyi a hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa. Ya kamata mu dukufa wajen habaka shirye-shiryen hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannonin kawar da talauci, samar da abinci, gina ababen more rayuwa da dai sauransu, da ba su goyon baya wajen aiwatar da ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063 da kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU ta tsara.

A jawabinsa, shugaban kasar Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa ya ce, ya nuna damuwa matuka kan kalubalen dake gabanmu ta fuskar tsarin ciniki tsakanin kasa da kasa, yana mai cewa, ya kamata kasashen BRICS su dukufa wajen kare tsarin cinikin tsakanin kasa da kasa. Ya ce, "A halin yanzu, bullar tsarin ciniki mai tallafawa bangare daya abun damuwa ne sosai, tsarin bai dace da manufar kungiyar cinikiyya ta duniya WTO ba, kuma mun damu sosai domin tsarin zai haddasa illa ga bunkasuwar tattalin arziki kasashe masu tasowa. Ya kamata mu yi tunani kan yanayin cinikayyar duniya a halin yanzu, musamman ma kan yadda za a inganta dauwamammen ci gaba da kuma neman ci gaba cikin yanayin fahimtar juna. A halin yanzu kuma, kasashen BRICS sun gane muhimmacin kafa wani tsarin cinikin tsakanin kasa da kasa cikin adalci, da fahimtar juna, ba tare da rufa-rufa ba, mai cike da 'yanci." (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China