Hausawa sun ce inda ranka ka sha kallo. Hamadar Kubuqi tamkar makaranta ce a gare ni, domin a kullum kara ganin abubuwa da fasasohin da ban taba gani ba nake. A yau na samu damar ganin wata fasaha ta adana tsirrai da iri, musammam tsirran da ba safai ake samunsu ba, da kuma wadanda ba sa rayuwa idan aka shuka su kai tsaye. Wato ana killace wadannan tsirrai ne a cikin kwalba dauke da ruwa, a wani daki mai tsafta da na'urori daidaita yanayi. Da farko dai, sai an cire musu duk wata kwayar cutar bacteria da bata jure yanayi mai tsanani, sannan daga bisani a shigar da su dakin da ake killace su. Abu na biyu kuma da ya ban sha'awa shi ne, wata rumfar gona da ake shuka tsirrai daban-daban masu jure yanayin Hamada a nahiyoiyi da yankuna daban-daban na duniya kamar nahiyar Afrika da Amurka da gabas ta tsakiya da sauransu. (Faeza Mustapha)