in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Afrika ta kudu sun cimma matsaya daya kan raya dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni
2018-07-25 13:53:58 cri

A jiya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa a Pretoria, hedkwatar kasar. Yayin ganawar tasu, shugabannin biyu sun jinjinawa zumunci dake tsakanin kasashen biyu, tare da cimma matsaya kan raya dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a sabon karni, da kara tuntuba tsakanin manyan jami'an bangarori daban, da zurfafa amince da juna a fannin siyasa, da yin musanyar ra'ayi kan raya kasa, da sa kaimi ga hadin kai, da zurfafa mu'ammalar al'adu, ta yadda jama'ar kasashen biyu za su amfana.

A safiyar jiya ne agogon Afirika ta kudu, shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya tarbi takwaransa na kasar Sin Mista Xi Jinping a harabar fadar shugaban kasar. Kuma shugabanni biyu da uwar gidansu sun kalli faretin ban girma da sojojin badugala suka shirya musu.

Bayan bikin nuna maraba, shugabannin biyu sun yi shawarwari tare da zanta da manema labarai, don bayyana ci gaban da suka samu a shawarwarin nasu. Xi Jinping ya nuna cewa, Sin da Afrika ta kudu kasancewar kasashe maso tasowa mafi muhimmanci da sabbin kasuwanni, bangarorin biyu na da dankon zumunci mai karfi da amincewa da juna tamkar aminan juna. Ya ce:

"Bana shekaru 20 ke nan da kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. A cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, mun nuna sahihanci da amincewa da juna da kuma dukufa kan samun bunkasuwa cikin hadin kai da kawo moriyar juna. Matakin da ya kai daga matsayin dangantakar dake tsakaninmu zuwa dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkanin fannoni. A halin yanzu dai, an shiga sabon zamani na raya tsarin mulkin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin, Afrika ta kudu kuma ta shiga sabon mataki na raya kasar, matakin da ya sa dangantar kasashen biyu shiga wani sabon babi."

Xi Jinping ya nuna cewa, sun samu ci gaba mai armashi a shawarwarin sa da shugaba Ramaphosa, sun kuma kai ga cimma matsaya kan raya dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a sabon zamani. Ya kamata bangarorin biyu sun kara amincewa da juna a siyasance, da kara hada kai bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kara tuntubar juna ta fuskar tsare-tsaren samun bunkasuwa, da zurfafa hadin kai a wasu sabbin fannoni na tattalin arziki, da kara tuntubar juna a fannin al'adu da dai sauransu. Ya nanata cewa:

"A matsayinsu na kasashe masu tasowa mafi girma da sabbin kasuwanni a duniya, Sin da Afrika ta kudu na da matsaya iri daya kan wasu manyan batutuwan kasa da kasa. Ya kamata bangarorin biyu su kara hada kansu don nuna goyon baya ga manufar kasancewar bangarori daban-daban a duniya, da kiyaye tsarin ciniki tsakanin bangarori da dama, da kokarin samar da tsarin dimokuradiyya tsakanin kasa da kasa da kiyaye muradun bai daya na Sin da Afrika ta kudu har ma da Sin da Afrika da na kasashe maso tasowa."

A nasa bangare, shugaba Ramaphosa ya ce, a cikin wadannan shekaru 20 tun bayan kafuwar dangantakar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, dangantakar dake tsakaninsu na kara samun bunkasuwa, wadda ke da muhimmanci sosai, kuma hadin kai a tsakaninsu na samun ci gaba kwarai da gaske. Matakin da ya amfanawa jama'ar kasahen biyu matuka, ya ce:

"Ni da shugaba Xi mun kai ga cimma matsaya daya kan marawa juna baya karkashin laimar MDD da sauran tsarin kasa da kasa. Ina godiya sosai kan goyon bayan da Sin take nunawa kasarmu don ganin mun rike matsayin mambar kwamitin sulhu na MDD da ba na dindinidn ba. Daga shekarar 2019, Afrika ta kudu za ta rike wannan matsayi, ina fatan hada kai da kasar Sin don ganin MDD ta ba da gudunmawarta yadda ya kamata cikin harkokin duniya."

Baya ga ziyarar shugaba Xi a wannan karo, zai kuma halarci taron kolin BRICS karo na 10 da za a yi a birnin Johannesburg. Xi ya ce, wannan taro na da muhimmanci sosai wajen kara hadin kai tsakanin kasashen BRICS, ya kamata bangarori daban-daban su yi amfani da wannan zarafi mai kyau don inganta dangantakar dake tsakaninsu da ba da gudunmawarsu wajen raya tattalin arzikin duniya na bude kofa.

Ban da wannan kuma, Xi Jinping ya ce, hadin kai da kasashen Afrika tsari ne da Sin ta kan bi cikin dogon lokaci wanda ba za ta yi watsi da shi ba ko kadan, kuma ya yi imanin cewa, taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika da za a gudanar a watan Satumba zai zama gagarumin biki wajen kara hadin kan Sin da Afrika. Kuma Shugaba Ramaphosa yana fatan halartar wannan taro mai muhimmanci. (Amina Xu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China