in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na Ruwanda
2018-07-24 13:18:00 cri

Jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Ruwanda Paul Kagame a birnin Kigali, fadar mulkin kasar Ruwanda, inda shugabannin biyu sun yaba matuka kan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma kyawawan sakamakon da aka samu cikin shekaru 47 da suka gabata, watau bayan kulla huldar diflomasiyya a tsakanin Sin da Ruwanda a shekarar 1971. Sa'an nan, sun tsara makomar hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, inda suka cimma matsaya kan raya hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu domin cimma moriyar juna, da kuma kara tallafawa al'ummomin kasashen nasu

Yanzu ga karin bayani da Maryam Yang ta hada mana:

A safiyar ranar 23 ga wata ne, shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya shirya bikin maraba da zuwan shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasar Ruwanda a dandalin dake gaban fadar shugaban kasa. Al'ummomin kasar sun taru a gefen titi suna yiwa motar dake dauke da shugaba Xi maraba a lokacin da take kokarin shiga fadar shugaban kasar, suna shewa cewa, maraba da zuwan bako mai martaba.

Daga bisa ni ne, shugabannin biyu suka fara shawarwari a tsakanin, inda Xi Jinping ya bayyana cewa, "Ina matukar farin cikin yin shawarwari tare da mai girma shugaba Kagame a birnin Kigali. Ka cimma nasarar ziyarar aiki da ka kai birnin Beijing na kasar Sin a watan Maris na shekarar da ta gabata, inda muka yi shawarwari mai zurfi da kuma kyau kwarai da gaske. A lokacin ne kuma, ka gayyace ni na kawo ziyara a kasarka, yanzu na zo, na cika alkawari. "

Haka kuma, shugaba Xi ya ce, a watan Maris na shekarar da ta gabata, shi da shugaba Kagame sun cimma matsaya kan yadda za a raya dangantaka da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, kasar Sin tana son hada kai da kasar Ruwanda domin karfafa dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a tallafawa al'ummomin kasashen biyu yadda ya kamata, da daga dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangare, Mr. Kagame ya ce, kasar Sin babbar animiyar kasashen Afirka ce, raya dangantakar abokantaka da kasar Sin yana da muhimmanci ga kasar Ruwanda, har ma ga kasashen Afirka baki daya. Kasarsa tana son yin shawarwari da kasar Sin kan tafiyar da harkokin kasa da kuma kara hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu don cimma moriyar juna.

Bugu da kari, ya ce, shawarar "Ziri daya da hanya daya" ta kasance kyakkyawar dama ga kasar Ruwanda da ma sauran kasashen Afirka, kasarsa tana son kara hadin gwiwa da bangarorin da abin ya shafa bisa shawarar. Kuma yana sa ran halartar taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da za a yi a birnin Beijing, da kuma ba da gudummawa yadda ya kamata domin cimma nasarar gudanar taron.

Ya ce, "Na yaba matuka kan dangantakar abokantaka dake tsakanin Sin da Ruwanda, da kuma babbar gudummawar da kasar Sin take bayarwa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Afirka. Muna fatan taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da za a yi a watan Satumba mai zuwa zai samar da wani dandali mai kyau gare mu wajen inganta hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da kuma kara tallafawa al'ummomin kasashen biyu."

Baya ganawar tasu, Xi Jinping ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, shi da shugaba Kagame sun yi musayar ra'ayoyi kan huldar dake tsakanin Sin da Ruwanda, taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da sauran batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, inda suka cimma matsaya kan abubuwa da dama. Shugaba Xi ya jaddada cewa, "Akwai muhimmiyar dama ta karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Ruwanda, ya kamata bangarorin biyu su karfafa fahimtar juna dake tsakaninsu a fannin siyasa, da kuma nuna goyon baya ga juna a fannin hanyar neman bunkasuwa da ta dace da yanayin da kasashen biyu suke ciki, da sauran batutuwan da ke janyo hankulansu. Muna ganin cewa, akwai bukatar karfafa shawarwari tsakanin kasashen biyu kan manufofin neman ci gaba, habaka hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a fannonin zuba jari, ciniki da kuma gina ababen more rayuwa da sauransu, ta yadda za a kara tallafawa al'ummomin kasashen biyu. Haka kuma, kasar Sin tana maraba da kasar Ruwanda da ta shiga cikin hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya."

Bayan ganawar tasu, shugabannin biyu sun kalli a kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, da suka hada da raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China