in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban Sin a kasashen Afirka
2018-07-26 09:40:11 cri

Daga ranar 21 zuwa 22 ga watan Yulin wannan shekarar ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping. Ya fara ziyarar aiki a kasar Senegal, ziyara ta farko da shugaba Xi zai kai ziyara kasar dake yammacin Afirka, kuma ziyarar farko da shugaban zai kai tun bayan da aka sake zabe shi shugaban kasar Sin a watan Maris na bana. A gabannin ziyarar, jakadan kasar Sin dake Senegal Zhang Xun ya bayyana cewa, kasar Sin ta zabi kasar Senegal a matsayin zangon farko na ziyarar aiki a Afirka, wannan ya nuna cewa, shugaba Xi da kasarsa sun dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakanin Sin da Senegal. Ya kuma nuna imanin cewa, ziyarar za ta ciyar da dangantakar abokantaka ta hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni gaba, kana za ta kara samar da alheri ga jama'ar kasashen biyu.

A 'yan shekarun baya bayan nan, kyakkyawar alakar dake tsakanin Senegal da Sin na kara inganta, inda tuni sassan biyu suka fara amfana da sakamakon dangantakar tasu. An kuma gudanar da ayyukan hadin gwiwa da dama, yayin da yanzu haka ake ci gaba da aiwatar da wasu sabbin ayyukan yadda ya kamata.

Haka kuma kasashen biyu na karfafa amincewar juna ta fuskar siyasa, da kuma alakar dake akwai tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Ya zuwa karshen shekarar 2017, yawan jarin da kasar Sin take da shirin zubawa a Senegal ya kai dalar Amurka miliyan 320. Kana yawan jarin da Sin ta riga ta zuba a kasar kai tsaye ya kai dalar Amurka miliyan 110, adadin da ya karu da kaso 120 bisa dari bayan shekara guda. A daya hannun kuma shugaba Xi ya kai ziyara kasar Rwanda da Afirka ta kudu, abin da kara nuna kyakkyawar alakar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka. (Ahmed, Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China