in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarata a Kubuqi 2
2018-07-23 15:37:45 cri

Yayin da nake kara kwanaki da ziyara a wannan yankin Hamada ta Kubuqi, ina kara ganin abubuwa masu daukar hankali. Abun da ya ja hankalina a yau shi ne yadda ake hada aikin yaki da Hamada da kuma kawar da taulauci da kyautata rayuwar masu karamin karfi. Wannan aiki ne da ya kunshi Gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da kuma mazauna yankunan.

Misali, a daya daga wuraren da naje, na ga yadda wani kamfani mai suna Elion dake samar da wutar lantarki daga hasken rana ya ba manoma aikin kula da faifan samar da lantarki daga hasken rana wato solar panels, da kuma damar yin shuke-shuke a kasan faifan da kiwon kaji da agwagi. Wato a nan an yi kokarin daidaita yankin Hamada, domin faifan ma an kafa su ne ta yadda za su kare Hamada daga kara ta'azzara, da samar da lantarki daga makamashi mai tsafta, kuma wutar lantarki da aka samar ta kai KWH miliyan 500 a kowace shekara. Baya ga haka, manoma ma na samun Karin kudin shiga, daga remimbi dubu 10 a shekara, zuwa remimbi dubu 50 ko 60 bisa ga ayyukan da aka samar musu.(Faeza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China