in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi da Sall sun halarci bikin mika filin wasan kokawa da Sin ta gina a Senegal
2018-07-23 11:11:52 cri

Jiya Lahadi ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Senegal Macky Sall suka halarci bikin mika filin wasan kokawa da Sin din ta gina a birnin Dakar, fadar mulkin kasar.

 A kan hanyar shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan zuwa filin wasan kokawa ta mota, dubban al'ummar kasar Senegal ne su ka yi layi a gefen titin domin murnar zuwansu, suna kada ganguna suna wake-wake, da raye-raye, don nuna farin ciki matuka da zuwan manyan bakin kasar Sin a kasarsu, tare da nuna babban yabo ga hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Senegal. Wasu kuwa sun rike kyallayen da aka rubuta kalaman "Zumuntar dake tsakanin kasashen Sin da Senegal za ta kara habaka" a hanayensu.

Yayin da shugabannnin kasashen biyu da uwargidansu suka shiga filin wasan kokawa, jama'ar dake wurin sun yi ta tafi, suna shewa, suna buga ganguna da kada tutocin kasashen Sin da Senegal tare da ma'aikatan kamfanin kasar Sin da suka shiga aikin gina filin wasan kokawar, domin gaida shugabannin kasashen biyu da uwargidansu.

A jawabinsa ministan ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Zhong Shan ya bayyana cewa, filin wasan kokawar da aka gina sabon sakamako ne da aka samu yayin da sassan biyu suke gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu, yana mai cewa, "Ziyarar aikin da shugaba Xi Jinping ke yi a nahiyar Afirka, ita ce ziyararsa a ketare ta farko a wannan shekarar da muke ciki, lamarin ya nuna cewa, yana mai da hankali matuka kan huldar dake tsakanin kasarsa da kasashen Afirka, Senegal ma tana kokari matuka kan aikin aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, haka kuma hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu yana kara karfafa, kasar Sin tana son hada kai tare da kasar Senegal domin ciyar da huldar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu gaba yadda ya kamata."

A nasa bangare, ministan ma'aikatar wasannin motsa jiki ta Senegal Matar Ba ya bayyana cewa, filin wasan kokawar da aka kammala zai biya bukatun 'yan wasan kasarsa, yana mai cewa, "Kasar Sin tana taimakawa kasarmu wajen gina wuraren wasannin motsa jiki, misali cibiyar wasan motsa jiki ta Zumunta, da wasu kananan cibiyoyin wasan motsa jiki a fadin kasar, yanzu haka an kammala aikin gina filin wasan kokawa a Dakar, ko shakka babu zai taka rawar gani wajen ci gaban wasan kokawa wanda shi ne wasan gargajiya na al'ummar kasar, cikin dogon lokaci, 'yan wasan kokawa na kasar ta Senegal da masu sha'awar wasan suna fatan za a gina wani filin wasan kokawa na sana'a a kasarsu, yanzu dai burinsu ya cika sakamakon goyon bayan amimansu na kasar Sin."

Yayin bikin mika filin, shugaba Xi ya mikawa takwaransa na Senegal Sall mabudin zinari na filin, daga baya shugabannin biyu da uwargidansu sun kalli nune-nunen fasahar wasan kokawar da 'yan wasan kasar suka shirya musu, bayan kammala nune-nunen, sun je filin wasa domin gaida da su.

Shugaba Xi ya yi nuni da cewa, filin wasan kokawar alama ce ta zumunta mai zurfi dake tsakanin al'ummun kasashen Sin da Senegal, kasar ta Senegal kasa ce mai cike da al'adu, kasar Sin tana son hada kai tare da Senegal domin kiyaye da kuma gadan al'adun gargajiyarsu.

Shugaba Sall shi ma ya bayyana cewa, wasan kokawa yana samun karbuwa a wajen al'ummun kasarsa, har ya kasance alamar al'adun kasar, a don haka ya nuna babbar godiya ga kasar Sin saboda taimakon da ta samar na aikin gina filin wasan kokawa na zamani, ana iya cewa, filin zai zama sabuwar alama ta sada zumunta dake tsakanin al'ummun sassan biyu.

Filin wasan kokawa yana wajen birnin Dakar, kuma wannan shi ne aiki mafi girma da kamfanin kasar Sin ya gudanar a kasar ta Senegal, kana shi ne filin wasan kokawa na zamani na farko da aka gina a nahiyar Afirka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China