in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Huldar tsakanin Sin da Afrika ta kudu ta zama abin koyi ga hadin kan kasashe maso tasowa
2018-07-23 10:14:37 cri

Shugaban kasar Sin Xi jinping zai kai ziyarar aiki a kasar Afrika ta kudu tare da halartar taron kolin BRICS karo na 10 da za a yi a birnin Johannesburg na kasar.

Jakadan Sin dake kasar Afirka ta kudu Lin Songtian ya shaidawa manema labaru cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta zama abin koyi ga hadin gwiwar kasashen masu tasowa.

Mista Lin ya ce, Sin da Afrika ta kudu sun bude hanyar jirgin sama kai tsaye, kuma galibin jiragen ruwan kasar Sin suna yada zango a Cape of Good Hope a kan hanyarsu ta zuwa Turai, kana wasu manyan hukumomin hada-hadar kudi na kasar Sin sun bude rassansu a Afrika ta kudu, ban da wannan kuma, Afrika ta kudu ta kasance kasar da ta fi karbi dalibai daga kasar Sin da kafa kwalejojin Confucius da kulla dangantakar abota tsakanin biranenta da kasar Sin, har ma ta shigar da harshen Sinanci a cikin manhajan karatunta

Lin Songtian ya ce, Sin ta farko a fanni ciniki da Afrika ta kudu cikin shekaru 9 a jere, kuma Afrika ta kudu ita ce babbar abokiyar cinikiyar kasar Sin a Afrika. Yawan kudin ciniki tsakanin kasashen biyu a shekarar bara ya kai dala biliyan 39.17, wanda ya ninka sau 26 kan na shekarar 1998, tun bayan da kasashen biyu suka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu.(Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China