in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya wallafa bayani a kafofin watsa labaru na kasar Afirka ta Kudu
2018-07-22 20:39:31 cri
A yau 22 ga wata, kafin ya kai ziyara a kasar Afirka ta Kudu, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya wallafa wani bayani mai taken "yin kokari tare don samar da sabon yanayi na sada zumunta a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu" a jaridun kasar Afirka ta Kudu wato "The Sunday Independent", "The Sunday Tribune", da kuma "Weekend Argus".

Xi Jinping ya bayyana cewa, bisa gayyatar da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya yi masa, yana jin farin ciki da ziyarar da zai kai kasar Afirka ta Kudu karo na 3 tare da halartar taron shugabannin kasashen kungiyar BRICS karo na 10.

Shekarar bana shekara ce da aka cika shekaru 20 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu, jama'ar kasashen biyu suna sada zumunta da juna a dogon lokaci. Bayan kafuwar sabuwar kasar Afirka ta Kudu, musamman a cikin shekaru 20 da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu, kasashen biyu suna nuna goyon baya da koyi da juna yayin da suke kokarin neman hanyar samun bunkasuwa mai dacewa. A cikin shekaru 6 da suka gabata, Sin da Afirka ta Kudu sun zama kasashen da suka shugabanci dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, sun yi hadin gwiwa da juna da sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare. A halin yanzu, dangantakar dake tsakanin Sin da Afrirka ta Kudu ta zama abin koyi na dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, da hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, da hadin gwiwar dake tsakanin kasuwanni masu tasowa, kana wannan yana da babbar ma'ana wajen raya burin bai daya na Sin da Afirka, da dangantakar dake tsakanin kasa da kasa ta girmama juna da adalci da hadin gwiwa da samun moriyar juna.

Shugabannin kasashen biyu suna ta yi mu'amala da juna, inda aka samu nasarori kan hadin gwiwar kasashen biyu a dukkan fannoni. Kasar Sin ta zama kasa ta farko da ta yi ciniki mafi girma a kasar Afirka ta Kudu a shekaru 9 a jere, kana kasar Afirka ta Kudu ta zama kasar ciniki mafi girma ta kasar Sin a nahiyar Afirka.

A shekarun baya baya nan, Sin da Afirka ta Kudu sun dauki matakai kamar yin bikin al'adun kasashen biyu, da kafa tsarin mu'amalar al'adu a tsakanin kasashen biyu, don sada zumunta da fahimtar juna a tsakanin jama'ar kasashen biyu. An fadada hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a fannonin bada ilmi, al'adu, kimiyya da fasaha, kiwon lafiya, matasa, mata da dai sauransu.

Yanzu, kasar Afirka na kan sabuwar hanyar sake raya kasa da neman ci gaban kasa, shugaba Cyril Ramaphosa ya gabatar da manufofi a fannonin raya tattalin arziki, kara samar da guraben aikin yi, kyautata zaman rayuwar jama'a, da inganta yin gyare-gyaren kan zaman al'umma da dai sauransu, ya kuma sanar da cewa, Afirka ta kudu ta shiga wani "Sabon zamani na cike da fata da imani". Muna son yin kokari tare da Afirka ta kudu, da amfani da damar cika shekaru 20 da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, don ciyar da dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni gaba.

Da farko, za a nuna amincewar juna a fannin siyasa tsakanin Sin da Afirka ta kudu zuwa wani sabon matsayi. Zamu ci gaba da yin mu'amala tsakanin shugabannin kasashen biyu, da kara hadin kai tsakanin jam'iyyu, da yin cudanya kan fasahohin da aka samu wajen gudanar da harkokin kasa, kana za a nuna fahimtar juna da goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar babbar moriyarmu da kuma wadanda ke jawo hankulanmu duka, za kuma mu zama abokai da 'yan uwa dake nuna amincewar juna har abada. Ina zura idon ganin ziyarar shugaba Cyril Ramaphosa a kasar Sin a watan Satumba a birnin Beijing, kuma zamu hada kai wajen shugabantar taron kolin Beijing na dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Na biyu, a inganta hakikanin hadin kai tsakanin Sin da Afirka ta kudu don samun sabbin nasarori. Ya kamata mu karfafa hadin kan kasashen biyu a fannin manyan tsare-tsare, kana da amfani da tsarin bangarori biyu, da dandalin tattaunawar hadin kan Sin da kasashen Afirka, da shawarar "Ziri daya da hanya daya", da tsarin hadin kan na BRICS da dai sauransu yadda ya kamata, da kuma zurfafa hadin kan kasashen biyu a wasu muhimman fannoni, ciki har da masana'antu, albarkatu, manyan kayayyakin more rayuwa, kudi, yawon shakatawa, tattalin arzikin na zamani da dai sauransu, ta haka za a kara samar da alherai ga jama'ar kasashen biyu.

Na uku, a kara inganta cudanyar al'adu a tsakanin Sin da Afirka ta kudu. Ya kamata mu yi amfani da tsarin cudanyar al'adu bisa babban mataki a tsakanin kasashen biyu, don kara yin mu'ammala a tsakanin al'ummomin kasashen biyu.

Na hudu, a inganta hadin kai bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Afirka ta kudu zuwa wani sabon matsayi. Ya kamata mu nuna goyon baya ga juna don shirya taron kolin Beijing na dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka na shekarar 2018, da tattaunawa karo na 10 na shugabannin kasashen BRICS, kana da kara yin daidaito da hadin kai bisa tsarin MDD, da na kungiyar G20, da na BRICS da dai sauransu, da kuma kiyaye babbar moriyar nahiyar Afirka da sauran kasashe masu tasowa.

Shekarar nan ta bana shekara ce ta cika shekaru 10 da aka soma yin tattaunawar shugabannin BRICS. Kasar Sin za ta nuna goyon baya sosai ga Afirka ta kudu don daukar bakuncin tattaunawar.

Shekarar da muke ciki kuma shekara ce ta cika shekaru 100 da aka haife marigayi Nelson Rolihlahla Mandela, wato shugaba na farko na sabuwar kasar Afirka ta kudu. Na yi imanin cewa, za a samu farfadowar Afirka ta kudu da duk nahiyar Afirka a wannan karni. Bari mu hada kai tare don bude sabon babi na sada zumunta a tsakanin Sin da Afirka ta kudu. (Zainab, Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China