in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarata a hamadar Kubuqi 1
2018-07-22 15:24:44 cri

Hamada kalma ce da zan iya cewa na saba da jinta kasancewata wadda ta fito daga yankin dake iyaka da yankunan Hamada wato sahara na Nahiyar Afrika. A matsayina ta 'yar asalin jihar Bornon Nijeriya, daya daga cikin wuraren kasar da ke fuskantar barazanar kwararowar Hamada, zan iya cewa sai yau na ga hamada a zahiri, duk da cewa ana kokarin yaki da ita, zan iya cewa ban taba ganin abun da ya kai ta kyau ba. A yayin da duniya ke kokarin daidaita yankunan Hamada, yau na ga jajircewa da kokarin kare muhalli a wajen al'ummar Sinawa. Yadda al'umma da Gwamnati suka tashi haikan wajen ganin sun kiyaye muhalli abun ban sha'awa ne, domin matakan da suka dauka, matakai ne dake haifar da riba da dama : wato daidaita yankunan Hamada ta hanyar dasa bishiyoyin da ke da juriya da yakarta, sannan kuma ake iya sarrafawa, wadanda ke samar da guraben aikin yi da kudin shiga.

Baya ga haka ga wurin shakawatawa, abubuwan da nake gani a zane ko talabaijin yau su na gani da idona, kamar cable way mai tafiya a sama da taimakon igiya da lantarki, ga kuma hawan ragumi, abun da ban taba tunanin zan iya ba saboda tsoro. Mafi ban sh'awa kuma shine motar tsere a Hamada wadda na ji kamar za ta kife da ni, sai dai abu ne da ban taba tunani ba, kuma ba zan taba mantawa ba. Lallai wannan rana ta shiga daya daga cikin muhimman tarihin rayuwata.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China