in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya kai ziyara ta farko a yammacin Afrika
2018-07-22 10:05:05 cri

Da yammacin jiya Asabar 21 ga watanYuli, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara ziyarar aikinsa a kasar Senegal. Shugabannin biyu sun yi ganawa tare da kuma gudanar da wani taron manema labarai, inda suka jinjinawa ci gaban da bangarorin biyu suka samu ta fuskar dangantakar dake tsakaninsu. Kuma sun cimma matsaya daya na kara yin hadin gwiwa don samun ci gaba ta fuskoki daban-daban da samar da wata dangantakar dake tsakaninsu mai kyau nan gaba. Shugaba Xi yayi maraba  da shugabanin kasashen Afrika ciki hadda shugaba Mackie SALL da su halarci taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin kai tsakain Sin da Afrika da za a yi a watan Satumba mai zuwa, inda za a tattauna kan manyan tsare-tsaren raya Sin da Afrika.

Macky SALL ya shedawa manema labarai cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na samun bunkasuwa sosai a halin yanzu, wadda kuma aka kafata bisa tushen taimakawa juna, mutunta juna da amincewa juna, kasashen biyu dai suna hadin kansu tare da yin shawarwari, ta yadda za a samu moriyar juna. Sin wata muhimmiyar kawa ce ta hadin kai, da kuma abota mai sahihanci.

Mista Xi ya kuma nuna cewa, ya kamata Sin da Senegal su kara hadin kai a fannin tsare-tsare da manufofi, da kuma sa kaimi ga hadin kai bisa tsarin shawarar "Ziri daya da hanya daya", kana da kara hadin kai a dukannin fannoni.

Game da hadin kan Sin da Afrika, shugaba Xi ya bayyana imaninsa kwarai da gaske, ya ce, bunkasuwar Sin na baiwa zarafi mai kyau ga nahiyar Afrika, shima bunkasuwar Afrika na samarwa kasar Sin karfi mai inganci. Beijing na daf da shirin gudanar da taron koli a watan Satumba mai zuwa. Taron dai na da jigon "Hadin kai da samun moriya tare da kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afrika", inda za a fitar da sabbin tsare-tsare da manufofi don kara hadin kai tsakanin Sin da Afrika. Xi yana sa ran ganawa da shugaba Macky Sall a birnin Beijing don tattaunawa kan wannan babban batu. Kuma ya yi imanin cewa, taron zai zama wani gagarumin biki ne wajen inganta hadin kan Sin da Afrika.

A nasa bangaren, Mista Macky Sall ya ce, Senegal na goyon bayan dandalin sosai, kuma tana sa ran zurfafa hadin kai tsakanin Sin da Afrika da kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afrika. Senegal kuma na fatan kara tuntuba da cimma maslaha da kasar Sin kan harkokin dake shafar bangarori daban-daban, da dukufa kan kafa wani tsarin duniya mai adalci, da daidaito tsakain bangarori da dama, ta yadda za a kiyaye tsarin tattauanwar harkoki tsakanin bangarori daban-daban da yaki da manufar kariyar ciniki cikin hadin kai.

Ban da wannan kuma, a wannan rana Mista Macky Sall ya samarwa shugaba Xi Jinping lambar yabo ta matsayin koli a Senegal, kuma shugabanni biyu sun amince da sanya hannu kan takardar hadin kai tsakain Sin da Afrika karkashin shawarar "Ziri daya da hanya daya". Hakan ya sa Senegal ta zama kasa ta farko da ta kulla irirn wannan dangantaka da kasar Sin. (Amina Xu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China