in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya wallafa wani bayaninsa a wata jaridar Rwanda
2018-07-21 17:55:01 cri
A yau 21 ga watan Yuli, a gabannin ziyararsa ta aiki a kasar Rwanda, an wallafa wani bayani mai take "Zumuncin Dake Kasancewa Tsakanin Sin da Rwanda Ya Fi Tsauni Tsayi" da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanya hannu a jaridar "New Era" ta kasar Rwanda.

A cikin bayaninsa, shugaba Xi Jinping ya ce, bisa gayyatar da shugaba Paul Kagame ya yi masa, zai kai ziyarar aiki kasar Rwanda tsakanin ranaikun 22 da 23 ga watan. Wannan ne karo na farko da ya kai ziyara kasar Rwanda, kuma karo na farko da wani shugaban kasar Sin ya kai ziyara kasar a tarihi. Sakamakon haka, yana sa ransa sosai ga ziyarar.

Shugaba Xi Jinping ya kuma nuna cewa, a 'yan shekarun baya bayan nan, bisa jagorantar shugaba Paul Kagame, gwamnati da al'ummar kasar Rwanda sun nuna himma da kwazo, sun yi namijin kokari, har ma sun ci nasarar samun wata hanyar bunkasa kasarsu dake dacewa da halayyar da kasarsu ke ciki.

Yanzu kasar Rwanda tana da kwanciyar hankali, alakar dake tsakanin gwamnati da al'ummarta tana cike da jituwa, har ma kome ya samu farfadowa da bunkasuwa. Zaman al'ummar Rwanda ma ya dade yana cikin zaman lafiya, tattalin arzikinta yana ta samun ci gaba cikin sauri. Sannan rawar da take takawa a yankin shiyya-shiyya har ma a duk duniya na samun karuwa. Yanzu ta kasance tamkar wani abin koyi ga sauran kasashen Afirka, har ma na duk duniya wajen sake samun bunkasuwar kasa. Shugaba Xi Jinping ya ce, yana farin ciki sosai ga wadannan sakamakon da kasar Rwanda ta samu, cikin sahihanci, shugaba Xi ya yi fatan kasar Rwanda za ta samu karin sabon sakamako a kan hanyar neman bunkasa.

Shugaba Xi Jinping ya kara da cewa, ko da yake kasar Sin da kasar Rwanda suna da nisa sosai tsakaninsu, kuma akwai bambanci da yawa tsakaninsu a fannonin girmansu da tsarin mulki da suke bi, da al'adunsu, amma zumuncin gargajiya ya dade yana kasancewa tsakanin al'ummomin kasashen biyu.

Shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, yanzu kasar Rwanda na nuna himma da kwazo wajen aiwatar da "shirin neman bunkasuwa nan da shekarar 2020". Sannan, kasar Sin ma na yin kokari ba tare da kasala ba, wajen cimma burukanta biyu, kafin a cika shekaru dari da kafuwar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin nan da shekarar 2021, kana kafin a cika shekaru dari daya da kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin nan da shekarar 2049. Sakamakon haka, hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen Sin da Rwanda tana da kyakkyawar dama. Sabo da haka, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wasu ra'ayoyinsa, kan yadda za a sanya sabbin abubuwa ga zumuncin gargajiya da hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban, da kuma kara bunkasa huldar dake tsakanin kasashen biyu har zuwa wani sabon mataki, da samun dimbin sakamakon a zo a gani domin kawo alheri ga al'ummomin kasashen biyu.

Da farko dai, ya kamata kasashen biyu su tsaya kan matsayin girmama juna, da kara amincewa da juna a fannonin siyasa. Babu tantama, bangaren Sin na tsayawa hanyar neman ci gaba da kasar Rwanda ta yadda za ta dogara ga kanta.

Sannan ya kamata kasashen biyu su hada shirye-shiryensu na neman ci gaba, da fadada fannonin da suke yin hadin gwiwa. Shugaba Xi Jinping yana fatan kasashen biyu za su kara yin hadin gwiwa a fannonin samar da ababen more rayuwar jama'a, da hakar ma'adinai da zuba jari da yin cinikayya, ta yadda zumuncin gargajiya dake kasancewa tsakanin kasashen biyu zai zama sakamakon hadin gwiwa irin na a zo a gani da zai iya haifar da moriyar al'ummominsu.

Na uku, ya kamata kasashen biyu su ingiza kansu wajen koyi da juna a fannin al'adun su, da kuma wadatar da fannonin musayar abubuwan dake shafar bil Adam. Ya kamata su kara yin hadin gwiwa da yin mu'amala a fannonin ba da ilmi, da al'adu da kiwon lafiya da sha'anin bude ido, da zirga-zirgar jiragen sama da dai makamatansu, ta yadda za a iya karfafa tushen zaman al'umma domin ci gaba da bunkasa huldar dake tsakanin kasashen biyu, hakan ta kai ga sanya zumuncin dake kasancewa tsakanin kasashen biyu ya samu aminci daga al'ummominsu.

Daga karshe dai, ya kamata kasashen biyu su yi mu'amala da kuma daidaita matsayinsu kan wasu batutuwan kasa da kasa. Kasar Sin ta yaba da kuma nuna goyon baya ga gudummawar da kasar Rwanda take bayarwa, a matsayin shugabar kungiyar hada kan kasashen Afirka wato AU, wajen tabbatar da hada kan kasashen Afirka, da ciyar da Afirka gaba. Ya kamata kasashen Sin da Rwanda su ci gaba da yin mu'amala da kuma daidaita matsayinsu kan wasu batutuwan kasa da kasa, da na shiyya-shiyya, domin tsayawa tsayin daka kan matsayin kare halaltattun muradun kasashe masu tasowa.

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya kara jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bin gaskiya, da nuna sahihanci, da zahiri da kuma zumunci da daidaiton ra'ayi kan batun adalci da na moriya, a lokacin da take kokarin kara yin mu'amala da sada karin zumunci, da fadada hadin gwiwa da dukkannin kasashen Afirka gaba daya, ciki har da kasar Rwanda.

Bayan wata guda da wani abu, za a shirya taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka na FOCAC a Beijing, shugaba Xi yana maraba da shugaba Paul Kagame ya halarci taron a matsayinsa na shugaban kasar Rwanda, kana shugaban karba karba na kungiyar AU, domin ci gaba da tattaunawa kan manufofin kara sada zumunta tsakanin Sin da Afirka. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China