in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen BRICS na neman ci gaba tare ta hanyar bin ka'idar hakurtar da juna
2018-07-20 12:26:19 cri

A tsakananin ranaikun 25 da 27 ga watan Yulin, za a shirya taron ganawa karo na 10 tsakanin shugabannin kasashen BRICS a birnin Johnnesberg na kasar Afirka ta kudu, bisa gayyatar da aka yi masa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ma zai halarci wannan taro, sannan zai kai ziyarar aiki kasar Afirka ta kudu. A gabannin ziyarar shugaba Xi Jinping, Mr. Lin Songtian, jakadan kasar Sin dake kasar Afirka ta kudu ya bayyana wa manema labaru fata da imaninsa kan wannan taron ganawa da makomar huldar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da kasar Afirka ta kudu. Jakada Lin Songtian ya nuna cewa, a yayin wannan taron kolin kungiyar BRICS, za a ji muryar kasashen BRICS ta tsaya kan hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban. Mr. Lin ya bayyana cewa, "Abu mafi muhimmanci shi ne fitar da muryar BRICS kan yadda suke kare ka'idar yin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, musamman tsarin yin cinikayya tsakanin bangarori daban daban a inuwar kungiyar cinikayya ta kasa da kasa, ko WTO a takaice. Kuma yadda suke gwagwarmayar yaki da ra'ayin daidaita batutuwa, da ra'ayin yin cinikayya bisa radin kan wani kadai. Na biyu shi ne kasashe biyar na BRICS za su yi musayar ra'ayoyinsu kan yadda suke daidaita hali mai sarkakiya da kasashen duniya ke ciki. Bugu da kari, za su kokarta kara amincewa da juna a fannin siyasa, domin kara yin hadin gwiwa tsakaninsu. Na uku kuma, wannan taron koli na BRICS, ya soma yin amfani da dama, da kalubalen da za su fuskanta, domin bunkasa masana'antu karo na 4. Babban jigon wanna taorn kolin shi ne 'a lokacin da ake bunkasa masana'antu karo na 4, ana yin kokarin hakurtar da juna, domin neman ci gaba da bunkasuwa tare' ".

Domin mayar da martani ga wannan jigo, kasar Sin da kasar Afirka ta kudu sun ba da shawarar "kafa huldar abokantaka irin ta juyin juya hali tsakanin kasashen BRICS, domin fuskantar sabon masanana'antun dake bullowa." Sauran mambobin kungiyar BRICS sun mayar da wannan martani sosai. Yanzu bangaren Sin da na Afirka ta kudu sun gaggauta tsara daftarin aiwatar da wannan shawara, sannan za a tattauna kan wannan daftari a yayin taron kolin BRICS.

Sannan jakada Lin Songtian ya bayyana cewa, a yayin taron kolin BRICS da aka shirya a watan Nuwamban bara, an kafa muhimmin harsashi ga wannan taro, wato an gabatar da salon yin hadin gwiwa kamar "BRICS da saura", wanda ya samu karbuwa sosai daga wajen sauran kasashe masu tasowa, musamman kasashen da tattalin arzikinsu ke samun karuwa cikin sauri yanzu, har ma da wasu manyan kasashen duniya. Jakada Lin ya kara da cewa, dukkanin kasashen Afirka suna sa ransu sosai ga wannan taron kolin BRICS, shugabannin kasashen Afirka 9 za su halarci wannan taron kolin, wannan kuma ya alamta cewa, tsarin kungiyar BRICS yana da imani, kuma yana bude kofarta, har ma yana hakurtar da saura.

A waje daya, jakada Lin Songtian ya nuna cewa, shigar da kasar Afirka ta kudu cikin kungiyar BRICS yana da muhimmanci sosai, ba ma kawai an habaka wakilci na BRICS ba, har ma an shigar da wani kyakkyawan karfi a ciki. Mr. Lin ya ce, "Yana da muhimmanci sosai shigar da kasar Afirka ta kudu a cikin BRICS. A farkon mataki, babu harafin S a cikin BRIC, sakamakon haka babu wata kasar Afirka a ciki. Shigar da kasar Afirka ta kudu ya alamta cewa, a lokacin da wakilcin BRICS ke samun kyautatu, ya kuma shafi bangarori daban daban, an kuma alamta cewa, kasashen BRICS na kokarin neman ci gaba bisa ka'idar hakurtar da saura. Kasar Afirka ta kudu kasa ce da ke bin ka'idodi sosai. A 'yan watannin nan, a lokacin da ake aiwatar da manufofin yin cinikayya maras 'yanci, da daidaita harkoki bisa muradun wata kasa kadai, a bayyane, kuma a fili take cewa, gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta bayyana matsayin ta na nuna adalci, domin kokarin kare adalci a duk duniya."

Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 20 da kafa huldar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da kasar Afirka ta kudu. Jakada Lin Songtian ya nuna cewa, a cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta samu ci gaba sosai, daga dangantakar abokantaka irin ta yau da kullum zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare tsare daga dukkan fannoni. Yanzu kasar Sin ta zama abokiyar cinikayya mafi girma ta kasar Afirka ta kudu a cikin shekaru 9 da suka gabata a jere. Kasar Afirka ta kudu ita kuma ta zama abokiyar cinikayya mafi girma ta kasar Sin a cikin kasashen Afirka cikin shekaru 8 da suka gabata a jere. Bugu da kari, yanzu Sinawa sun fi son zuba jari da kuma bude ido a kasar Afirka ta kudu. Bisa alkaluman da aka bayar, an ce, yawan jarin da kasar Sin ta zuba a kasar Afirka ta kudu ya kai dalar Amurka biliyan 25. Game da dalilan da suka sa kasashen biyu suka samu irin wadannan sakamakon a zo a gani, Jakada Lin Songtian ya bayyana cewa, "Da farko dai, kara yin mu'amala a lokacin da suke tsara manufofi. Manufofin da shugabannin kasashen biyu suka tsara sun ba da jagoranci sosai ga aikin yin mu'amala tsakanin al'ummomin kasashen biyu. Na biyu, tabbatar da yin cinikayya maras kaidi tsakanin kasashen biyun. Yawan kudin cinikayya da aka samu a tsakanin kasashen Sin da Afirka ta kudu ya kai dalar Amurka kusan biliyan 40, wato ya ninka sau 25 idan an kwatanta shi da na shekarar 1998. Na uku kuma, tabbatar da hade ababen more rayuwa na kasashen biyu. Yanzu haka jiragen ruwa da na sama na kasashen biyu, suna tafiya a tsakanin kasashen biyu kai tsaye. Na hudu an hade sassan hada hadar kudi. Yanzu muhimman hukumomin kudi na kasar Sin dukkansu sun kafa sassansu ko ofisoshinsu a birnin Johnnesberg na kasar Afirka ta kudu. Daga karshe, an yi kokarin kulla alaka tsakanin al'ummomin kasashen biyun. Inda a yanzu, yawan dalibai Sinawa wadanda suke karatu a kasar Afirka ta kudu ya haura na sauran kasashen Afirka. Sannan yawan larduna da jihohi da birane na kasar Afirka ta kudu, wadanda suka kulla zumunta da larduna da birane na kasar Sin ya haura na sauran kasashen Afirka, har ma adadin kwalejojin Confucius da aka kafa a kasar Afirka ta kudu shi ma ya zarce na sauran kasashen Afirka. Yanzu kasar Afirka ta kudu ta riga ta sanya harshen Sinanci, ya zama harshen da dole ne dalibanta su koya."

Lin Songtian ya kuma nuna cewa, shugaba Xi Jinping zai sake gudanar da ziyarar aiki a kasar Afirka ta kudu, sannan a karshen watan Agusta da farkon watan Nuwamba mai zuwa, shugaba Matamela Cyril Ramaphosa na kasar Afirka ta kudun, shi ma zai kai ziyarar aiki a kasar Sin, kuma za su shugabanci taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za a yi a Beijing. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China