in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Kasashen Larabawa Na Hadin Kai Wajen Kafa "Ziri Daya Da Hanya Daya" Domin Neman Moriya Da Nasara Tare
2018-07-19 20:16:43 cri
A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya fara ziyararsa a Hadaddiyar Daular Larabawa. Wannan ne karo na farko da ya kai ziyara kasashen waje tun bayan aka sake zabarsa shugaban kasar Sin a farkon bana, kana karo na farko da shugaban kasar Sin ya kai ziyara Hadaddiyar Daular Larabawa kusan shekaru 30 ke nan da suka gabata.

A shekarar 2012 ne, aka kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasar Sin da Hadaddiyar Daular Larabawa, lamarin ya sa Hadaddiyar Daular Larabawa ta zama kasar Larabawa ta farko a yankin tekun Fasha wadda ta kulla dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare. Sabo da haka, kasashen biyu sun yi amfani da wannan dama wajen karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban, har ma sun kaddamar da wasu ayyuka wadanda za su kawo sakamakon a zo a gani a Hadaddiyar Daular Larabawa. Daga cikinsu, hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin makamashi ta zama aiki mafi muhimmanci dake bayyana yadda kasar Sin da kasashen Larabawa dake yankin Gabas ta tsakiya suke yin hadin gwiwa a fannin samar da man fetur da iskar gas.

Bugu da kari, hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa a fannonin samar da ababen more rayuwar jama'a da na sadarwa da hada-hadar kudi da fannonin dake shafar bil Adama tana ta karfafuwa. Musamman bayan da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da shawarar bunkasa "ziri daya da hanya daya" a shekarar 2013, yarima Hamdan bin Mohammed bin Rashid Al Maktoum na Hadaddiyar Daular Larabawa ya mayar da martani cikin yakini, ya kuma nuna yabo sosai ga shawarar. An yi hasashen cewa, tabbas ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kai Hadaddiyar Daular Larabawa za ta daga hadin gwiwar kut da kut da kasashen biyu suke yi zuwa wani sabon mataki.

Karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da Hadaddiyar Daular Larabawa, zai ba da gudummawa wajen inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Gabas ta Tsakiya baki daya bisa shirin "ziri daya da hanya daya". Alkaluman kididdiga na nuna cewa, daga shekarar 1978 zuwa shekarar 2011, adadin cinikin dake tsakanin kasar Sin da kasashen Gabas ta Tsakiya ya karu da kashi 19.7 bisa dari cikin ko wace shekara, wanda ya wuce matsakaicin adadin karuwar ciniki dake tsakanin kasar Sin da kasashen ketare. Kana, hadin gwiwar harkokin makamashi ita ce muhimmin aiki na bangarorin biyu.

Yayin taron ministocin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa karo na 8 da aka yi a ranar 10 ga watan nan a birnin Beijing, shugaba Xi Jinping ya nuna fatan cewa, ya kamata kasar Sin da kasashen Larabawa su yi amfani da wannan dama ta kara musayar ra'ayoyi da hadin gwiwa a tsakanin bangarori biyu, domin zurfafa hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa a fannonin man fetur da iskar gas, makamashin da ba sa gurbata muhalli, ta yadda za a ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu gaba a fannin sha'anin hada-hadar kudi da na fasahohin zamani.

Haka kuma, shawarar "ziri daya da hanya daya" ya kasance kyakkyawar dama ga kasashen Gabas ta Tsakiya wajen neman ci gaba. Bangarorin biyu sun sha amincewa da buri daya wajen neman bunkasuwa da kuma taimakawa juna a fannoni daban daban, fuskantar makoma mai kyau wajen aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya". (Sanusi Chen, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China