in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Furucin jami'in Amurka ya saba gaskiya
2018-07-19 20:10:31 cri
Yau Alhamis ne a birnin Beijing, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying ta ce, Sin ta dade tana bayyana matsayinta a fili kan takaddamar cinikayyar dake tsakaninta da Amurka. Tun farko, Sin ta bayyana matsayinta haikan cewa, ba ta fatan yin yakin cinikayya da Amurka, amma ba ta jin tsoron yakin. Game da furucin wani jami'in Amurka, Madam Hua ta ce wannan ya saba da gaskiya, kuma abun ban mamaki ne.

Rahotannin da aka ruwaito sun ce, darektan kwamitin tattalin arziki na fadar White House ta Amurka, Larry Kudlow ya dorawa kasar Sin laifin rashin cimma yarjejeniyar daidaita sabanin cinikayya tsakanin Amurka da Sin. Kudlow ya ce, muddin Sin ta bullo da shiri mai gamsarwa, Amurka za ta dakatar da kara sanya harajin kwastam kan kayayyakin kasar Sin. Game da kalaman nasa, Madam Hua ta yi sharhin cewa, kasar Sin na nuna iyakacin sahihanci da hakuri don daidaita sabani ta hanyar yin shawarwari tare da Amurka, don kar rikicin ciniki ya tsananta. Duniya ta ji kalaman jami'in na Amurka, kuma kwata-kwata ya saba gaskiya, ya mai da baki fari, abu ne mai ban mamaki.

Madam Hua ta bayyana cewa, kamata ya yi Amurka ta fahimci cewa, a wannan karnin da muke ciki, ana kara samun dunkulewar tattalin arziki a duk fadin duniya, inda ta ce, kasar Sin na da imani da karfin kare 'yanci da muradunta, kuma za ta hada kai tare da sauran kasashe don kare ka'idojin kasa da kasa da kuma tsarin cinikayya dake kunshe da bangarori da dama. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China