in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban hukumar zartarwar AU ya bukaci shugabanni a duniya su yi koyi da Nelson Mandela
2018-07-19 10:49:25 cri
Shugaban hukumar zartarwar tarayyar Afrika AU, Moussa Faki Mahamat, ya bukaci shugabanni duniya su yi koyi da burin Nelson Mandela na tabbatar da daidaito da makoma ta bai daya.

Shugaban ya yi wannan kiran ne yayin da duniya ke bikin cikar Nelson Mandela shekaru 100 da haihuwa.

MDD ce ta ware ranar haihuwar Mandela wato 18 ga watan Yuli, a matsayin ranar tunawa da Mandela ta duniya, da nufin tunawa da rayuwarsa, wadda ta kasance abun misali da koyi ga daukacin al'umma.

Ta kuma yi kira ga dukkan al'ummar duniya su yi koyi tare da samun kwarin gwiwa daga jajircewa irinta Mandela, wajen kare hakkokin dan Adam da tabbatar da zaman lafiya da sulhu da daidaton jinsi da hakkokin yara da sauran masu rauni da kuma yaki da talauci da tabbatar da adalci a tsakanin al'ummu.

A shekarar 2013 ne AU ta ayyana shekarun dake tsakanin 2014 da 2024 a matsayin 'shekaru 10 na sulhu a Afrika na Nelson Mandela' ta na mai kira ga kasashe mambobinta su daukaka gaskiya da sulhu a matsayin hanyoyin inganta demokradiyya da shugabanci da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaban nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China