in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kalubalanci Trump da ya yi watsi da tsarin kara buga haraji
2018-07-18 13:52:25 cri

Jiya Talata 17 ga wata, shugaban kwamitin kudi na majalisar dattijai na majalisar dokokin kasar Amurka dake kula da harkokin sa ido kan manufofin cinikin kasar, kana mambar jam'iyyar Republic, Orrin Hatch, ya kalubalanci gwamnatin Donald Trump da ta yi shawarwari da abokan ciniki a maimakon tsarin kara buga haraji kan sauran kasashe, idan ba haka ba, zai baiwa majalisar shawarar kayyade ikonsa na ba da izini a fannin ciniki.

Hatch ya bayyana haka ne yayin da ya yi wani jawabi a majalisar dattijai ta Amurkar, ya ce gwamnatin Trump ta yi barazana ko kuma tabbatar da karawa sauran kasashe harajin dala biliyan 500, matakin da ya jefa jama'a da kamfanonin Amurka cikin hadari, tare da kawo illa ga ci gaban da aka samu ta fuskar kwaskwarimar manufar harajin, yanzu ana matukar bukatar shawarwari a fannin ciniki. Idan gwamnatin Trump ta nace ga tsarin kara harajin ba tare da yin tunani ga illar da hakan zai jawo ba, to zai sa kaimi ga majalisar dokokin kasar da ta kayyade ikon Trump na ba da izini a fannin ciniki. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China