in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugaban bankin duniya
2018-07-17 10:04:21 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban bankin duniya Jim Yong Kim, jiya Litinin a nan birnin Beijing. Yayin ganawar tasu, Mista Xi ya nuna cewa, bankin duniya wani karfi ne mai muhimmanci wajen kiyaye manufar ciniki tsakanin bangarori daban-daban da dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya, kuma Sin na fatan zurfafa dangantakar abota da bankin ta yadda za a kara samar da sauki ga harkokin ciniki da zuba jari, da rage talauci da samun ci gaba mai dorewa a duniya, da kuma raya tattalin arziki na bude kofa da raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan Bil Adama.

Xi Jinping ya jaddada cewa, bunkasuwar kasar Sin na amfana sosai daga tsarin dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya da ciniki cikin 'yanci, a sa'i daya kuma, ta ba da gudunmawarta yadda ya kamata ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Ya kara da cewa, Sin na yaki da zargin da ake yi mata ba tare da wata hujja ba, kuma za ta nace ga kiyaye moriyarta yadda ya kamata. Shugaba Xi ya ce Sin na fatan kara hadin kai da banki bisa shawarwarin "Ziri daya da hanya daya".

A nasa bangaren, Jim Yong Kim cewa ya yi, bankin duniya na yabawa sosai da goyon bayan da Sin take ba tsarin kasancewar bangarori da dama a duniya da dunkulewar tattalin arzikin duniya bai daya, da kuma goyon bayan bankin da ya kara jari da yin kwaskwarima kan tsarin hannun jari. Ya ce Bankin na fatan kara zurfafa hadin kai da kasar Sin bisa shawarwarin "Ziri daya da hanya daya", da kuma sa kaimi ga rage talauci da raya duniya. (Amina Xu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China