in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar Xi a kasashen Afirka za ta sanya sabon karfi ga hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka
2018-07-13 19:47:29 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gudanar da ziyarar aiki a kasashen hadaddiyar Daular Larabawa, da Senegal, da Ruwanda, da kuma Afirka ta Kudu, tsakanin ranekun 19 zuwa 24 ga wannan wata na Yuli, kuma zai halarci taron ganawa tsakanin kasashen mambobin BRICS karo na 10, wanda za a shirya a Johannesburg, tsakanin ranekun 25 zuwa 27 ga watan Yulin da muke ciki. Bayan kammala dukannin ayyukan, shugaba Xi zai yada zango a kasar ta Mauritius, inda zai gudanar da ziyarar sada zumunta.

Wannan ita ce ziyara mai muhimmanci da shugaba Xi zai yi a sabon muhallin tarihi na yanzu, kuma ko shakka ba bu tana da babbar ma'ana wajen ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasashen mambobin kungiyar BRICS, da hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, haka kuma tana da babbar ma'ana wajen ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa.

Ziyarar da shugaba Xi zai yi a Afirka, ita ce ta hudu a nahiyar a cikin shekaru biyar da suka gabata; wato tun bayan da ya hau kan mukaminsa na shugaban kasar Sin.

A halin da ake ciki yanzu, kasashen duniya sun gamu da sabbin kalubale yayin da suke kokarin raya siyasar kasa da kasa, da tattalin arzikin duniya; Misali a nan shi ne batun kariya ga cinikayya, da gudanar da cinikayyar kashin kai, ana kuma damuwa kan makomar cinikayyar duniya. Har kullum kasar Sin tana mai da hankali kan kasashen Afirka, kuma tana sanya kokari matuka kan ci gaban kasashen. Ko shakka babu ziyarar da shugaba Xi Jinping zai kai a nahiyar za ta sa kaimi kan ci gaban kasashen Afirka, tare kuma da sanya sabon karfi, ga hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu wato Sin da Afirka.

Kawo yanzu an riga an samu babban sakamako, yayin da ake gudanar da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, musamman ma a fannin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya. Tun daga shekarar 2009 har zuwa yanzu, kasar Sin ta kasance abokiyar cinikayya mafi girma ta kasashen Afirka. A shekarar 2017, adadin cinikayyar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka ya kai dalar Amurka biliyan 170, kana adadin jarin da kasar Sin ta zuba ga kasashen Afirka kai tsaye ya kai dalar Amurka biliyan 40. An yi hasashe cewa, a cikin shekaru goma masu zuwa, kasar Sin za ta kasance kasa mafi girma wadda ta zuba jari a kasashen Afirka a maimakon kasashen yamma, wadanda suka gudanar da cinikayya a nahiyar har tsawon shekaru daruruwa.

Kana an samu sakamako a kasashen Afirka, yayin da ake aiwatar manufar ziri daya da hanya daya; Misali layin dogon da aka gina tsakanin kasar Habasha da Djibouti, da layin dogon da aka gina tsakanin Mombasa da Neirobi a kasar ta Kenya wadanda sun riga sun fara aiki. Ana iya cewa, sassan biyu sun samu babban ci gaba a fannonin gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a, da gudanar da cinikayya da kuma harkar kudi.

Ban da haka, cudanyar siyasa dake tsakanin Sin da Afirka tana kara zurfafa sannu a hankali. Yanzu haka sassan biyu sun cimma matsaya guda wajen raya ci gabansu, kuma wasu kasashen Afirka na zuwa nan kasar Sin kai tsaye domin koyon fasahahin raya kasa da kasar Sin ta samu, kuma manyan jami'an na kasashen Afirka su ma na zuwa Sin domin samun horo.

Hakazalika, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a fannin samar da tsaro shi ma ya samu sabon ci gaba. Kawo yanzu sojojin kasar Sin kusan 2500 suna gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya a kasashen Sudan ta Kudu, da Mali da sauran kasashe, adadin da ya kai kaso 80 bisa dari na daukacin sojojin kiyaye zaman lafiyar da kasar Sin ta tura a sassan fadin duniya.

A watan Satumban shekarar 2015, yayin babban taron MDD, shugaba Xi ya sanar da cewa, kasar Sin za ta samar da dalar Amurka miliyan 100 a cikin shekaru 5 masu zuwa, domin gina rundunar sojojin tarayyar Afirka wato AU, tare kuma da gina rundunar sojojin ko ta kwana na kiyaye zaman lafiya ta MDD wanda da hakan adadin dakarun ta zai kai 8000.

Daga ziyarar da shugaba Xi da sauran manyan jami'an kasar Sin suka yi a kasashen Afirka, da matakan da kasar Sin ta dauka domin kara ingiza hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka, ana iya gano cewa, duk da cewa yanayin duniya ya yi manyan sauye-sauye, har kullum kasar Sin tana goyon bayan aminanta na kasashen Afirka.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China