in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta cimma sakamako da dama bisa manufar sabunta fasahohi don neman ci gaba
2018-07-11 12:29:53 cri

Jiya Talata, kungiyar kare ikon mallakar fasaha ta duniya ta fidda rahotonta na shekarar 2018. Cikin rahoton, kasar Sin ta kara samun ci gaba daga matsayi na 22 a shekarar 2017 zuwa matsayi na 17 a bana a wannan fanni, kuma Sin ita ce kasa daya tilo dake cikin kasashe masu samun matsakacin kudin shiga, wadda take cikin jerin kasashe guda 20 dake sahun gaba a wannan fanni. Kana, ita ce kasa daya dake cikin kasashe masu samun matsakaicin kudin shiga, wadda ta ci gaba da rage bambancin dake tsakaninta da kasashe masu samun ci gaban tattalin arziki a wannan fanni na sabunta fasahohi. Lamarin ya nuna manyan sakamakon da kasar Sin ta samu bisa manufarta ta sabunta fasahohi don neman ci gaba mai inganci.

Ga karin bayani da Maryam Yang ta hada mana:

A shekarun baya bayan nan, kasar Sin ta ci gaba da samun ci gaba a fannin sabunta fasahohi. Tun daga shekarar 2012 da aka gudanar da babban taron wakilan JKS karo na 18, ya zuwa yanzu, gaba daya kasar Sin ta sami daga matsayinta har sau 17 cikin jerin kasashen dake neman sabunta fasahohi, lamarin da ya nuna sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin sabunta fasahohi domin neman ci gaba mai inganci. Babban sakataren kungiyar kare ikon mallakar fasaha ta duniya Francis Gurry ya bayyana cewa, cikin 'yan shekarun nan, kasar Sin ta samu ci gaba matuka a fannin sabunta fasahohi, saboda Sin ta mai da hankali matuka kan wannan aiki. Haka kuma, manufar sabunta fasahohi domin neman ci gaba da kasar Sin ta bullo da ita, tana daukar batun "sabuntawa" a matsayin aiki mai muhimmanci ta fuskar neman ci gaban tattalin arziki, kana kasar Sin ta tsara da aiwatar da shirye-shiryen da abin ya shafa yadda ya kamata, dalilin da ya sa, Sin tana ci gaba da zuba karin kudade domin sabunta fasahohi da kuma gabatar da karin bukatar mallakar fasaha, hakan ya sa, Sin ta sha gaban sauran kasashe a duniya. Ya kara da cewa, "a ganina, manufar sabunta fasahohi don neman ci gaba ita ce manufar da ta mai da aikin neman sabuntawa a matsayin cibiyar aikin neman bunkasuwa, wadda kuma ta tabbatar da nasarar da kasar Sin ta samu."

Haka kuma, ya ce, a halin yanzu, ana samun sauyi a tsarin tattalin arziki daga mai dogaro kan masana'antun sarrafa kayayyaki zuwa mai dogaro kan harkokin fasaha, kuma sabunta fasahohi zai tabbatar da cimma nasarar kasar Sin kan wannan sauyi. Ya kuma shawarci kasar Sin cewa, ya kamata ta tsaya tsayin daka kan wannan manufa, saboda sakamakon da kasar Sin ta riga ta cimma sun nuna daidaiton wannan manufa.

Sa'an nan kuma, da yake tsokaci kan zargin da aka yi wa kasar Sin ta fuskar kare ikon mallakar fasaha, Mr. Gurry ya ce, babu wata kasa a duniya, wadda ba ta da kuskure a wannan aiki, ana iya cewa, kasar Sin tana kokari kan aikin kare ikon mallakar fasaha, ko da Sin ba ta fidda dokar kare ikon mallakar fasaha a farko ba, wato ba ta samu dokar ba har zuwa shekarar 1984. Amma cikin shekaru kimanin 40 da suka gabata, kasar Sin ta bullo da wani tsarin kare ikon mallakar fasaha da ya dace da ci gaban duniya. Ya ce, "a ganina, kasar Sin ta yi aiki mai kyau a wannan fanni, kamfanonin kasar Sin sun cimma sakamako da dama, kuma Sin ita ce kasa ta biyu a fannin adadin bukatar neman mallakar fasaha. Haka kuma, kasar Sin ita ce muhimmiyar kasa mai samar da sabbin fasahohi a duniya, wannan shi ne dalilin da ya sa, kasar Sin ta kan mai da hankali matuka wajen kare ikon mallakar fasaha cikin kasuwannin gida da na ketare."

A nasa bangare, jakada Yu Jianhua, zaunannen wakilin kasar Sin dake ofishin MDD a birnin Geneva, da kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland, ya ce, babban ci gaban da kasar Sin ta samu kan aikin sabunta fasahohi cikin shekaru 40 da suka gabata, ya nuna kwarewar kasar Sin wajen neman ci gaba mai inganci ta hanyar sabunta fasahohi.

Haka kuma, ya ce, "karfin kasar Sin wajen sabunta fasahohi yana taimakawa kasar wajen neman ci gaba mai inganci, ya kamata mu ci gaba da bin manufar sabunta fasahohi don neman ci gaba, karfafa kare ikon makallar fasaha da kuma inganta hadin gwiwar kasa da kasa, domin cimma burinmu na raya kasa da kuma gina wata kasa mai wadata. Amma duk wanda yake son hana bunkasuwar Sin a wannan fanni, Sin ba za ta yi hakuri ba. Sabo da wajibi ne kasar Sin ta kare matsayin da 'yancinta na sabunta fasahohi, da kuma 'yancinta na neman raya kanta cikin lumana" (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China