Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Thailand ya tabbatar da cewa, ya zuwa karfe 9 na safiyar jiya Lahadi agogon wurin, Sinawa 41 ne suka rasa rayukansu sakamakon hadarin kifewar kwale-kwale a tsibirin Phuket dake kasar Thailand. Kawo yanzu, hadarin ya yi sanadin mutuwar mutane 42, kana wasu 14 kuma sun bace.
Jiya Lahadi da safe, kungiyoyi biyu dake aikin ceto daga kasar Sin ne suka fara gudanar da ayyukan ceto. Masu aikin ceton suna amfani da na'urorin musamman don gudanar da ayyuka a yankin ruwan tekun da hadarin ya auku.(Murtala Zhang)