Bisa ga daftarin, masu zuba jarin da za su iya sayen hannayen jari nau'in A a kasar Sin sun hada da mutanen kasashen waje dake aiki a kasar Sin da kuma mutanen kasashen waje da suka kasance ma'aikatan kamfanonin dake sayar da nau'in hannayen jari wadanda kuma suke aiki a wajen kasar Sin.
Hukumar kula da takardun hada-hadar kudi ta kasar Sin ta bayyana cewa, matakin na iya kara fadada hanyoyin jari ga kasuwannin hada-hadar kudi ta kasar Sin, tare da kyautata tsarin kasuwannin. Sa'an nan, zai kara bude kasuwannin hada-hadar kudi ta kasar Sin ga kasashen duniya, kuma hakan na da muhimmiyar ma'ana.(Lubabatu)