in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yakin cinikayya zai lahanta moriyar Amurka a fannoni biyar
2018-07-08 17:07:11 cri

Tun daga watan Maris na bana, kasashen Sin da Amurka suke fama da rigingimun cinikayya, wanda ke kawo rikici ga tattalin arzikin duniya, ko shakka babu yakin cinikayyar zai lahanta babbar moriya ta sassan biyu.  

Idan Amurka ta nace ga tayar da yakin cinikayya, to za ta rasa babbar moriyarta a fannoni biyar.

Na farko, yakin cinikayyar zai kawo mummunan tasiri ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Amurka a nan gaba, bisa sakamakon da cibiyar nazarin cinikayya ta Peterson ta samu a shekarar 2013, an ce, idan Sin da Amurka suka gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu yadda ya kamata, adadin cinikin da za su samu zai karu har ya kai dalar Amurka biliyan 500, tare kuma da kara samar da guraben aikin yi miliyan 4 da dubu 800.

Na biyu, yakin cinikayya zai sa kasashen biyu wato Sin da Amurka su rasa babbar moriyarsu. Idan Amurka ta yiwa kasar Sin takunkumi bisa rahoton binciken sashe na 301 da ta yi, to hakan zai katse cudanyar dake tsakanin ayyukan samar da kayayyaki na kasashe a fadin duniya, sakamakon haka, ba ma kawai lamarin zai kawo tasiri ga Sin da Amurka bane, har ma zai kawo tasiri ga sauran kasashen duniya.

Na uku, yakin cinikayya zai sa kasashen duniya su rasa babbar damar tarihi ta farfadowar tattalin arziki. Tun daga shekarar 2017, tattalin arzikin duniya ya fara farfadowa sannu a hankali, musamman ma tun farkon bana, tattalin arzikin duniya ya samu ci gaba a bayyane, idan ba a daitaita matsalar yakin cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka ba, to, farfadowar tattalin arzikin duniya zai iya gamuwa da kalubale, wasu hukumomin nazari kan tattalin arzikin duniya sun yi hasashe cewa, mai yiwuwa ne yakin cinikayyar zai sa adadin cinikin duniya ya ragu har da kaso 40 bisa dari, ko shakka babu babbar masifa ce ga daukacin kasashen duniya baki daya.

Na hudu, yakin cinikayyar zai kawo tasiri ga kwarjinin tsarin kasashen duniya wanda aka kafa kafin shekaru da dama da suka gabata, har zai sa tattalin arzikin duniya ya shiga mawuyacin hali. A halin da ake ciki yanzu, hukumar ciniki ta duniya wato WTO, ita ma tana fama da matsala mai tsanani, har wasu jakadun kasashen duniya dake wakilci a hukumar sun nuna damuwa kan batun. Hakika tun daga shekarar 1974, Amurka ta taba sanyawa kasashe 35 takunkumi har sau 125 bisa rahoton bincike na sashe na 301 da ta yi, ya zuwa shekarar 1995 da aka kafa hukumar WTO, hukumar ta nuna kiyayya ga Amurka, inda ta bayyana cewa, matakin da Amurka ta dauka bai dace da ka'idojin WTO ba, a don haka tun daga wannan shekarar, Amurka ta daina yin amfani da rahoton binciken, amma yanzu Amurka ta sake yin amfani da rahoton binciken sashe na 301 domin kaddamar da takunkumi ga kasar Sin, tabbas ne zai kawo babban kalubale ga tattalin arzikin duniya da tsarin duniya da kuma ka'idojin duniya.

Na biyar, yakin cinikayya zai sa Amurka ta rasa babbar ribar da zata samu daga bangaren kasuwar kasar Sin, yanzu kasuwar kasar Sin tana samun ci gaba cikin sauri, kusan ta kai matsayin na Amurka a shekarar 2017, kana an yi hasashe cewa, ci gaban kasuwar kasar Sin zai karu da kaso 13 bisa dari a ko wace shekara, da haka za ta kai sahun gaba a duniya bada dadewa ba, a sa'i daya kuma, a cikin shekaru biyar masu zuwa, adadin kudin da kasar Sin zata samu daga wajen shigo da kayayyaki daga kasashen ketare zai karu har da dalar Amurka biliyan dubu goma. Shi ya sa ana iya cewa, yakin cinikayyar zai sa Amurka ta rasa babbar ribar da zata samu daga bangaren kasuwar kasar Sin

To idan Amurka ta canja tunaninta, hakika sassan biyu wato Sin da Amurka zasu samu babban sakamako a fannoni biyar.

Da farko dai, idan Amurka ta saukaka sharadin fitar da kayayakin da ake samarwa ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani zuwa ga kasar Sin, zata samu riba mai tsoka daga wajen. Na biyu, idan Sin da Amurka suka kara sa kaimi kan hadin gwiwar tattalin arziki ta yanar gizo, to akalla adadin kayayyakin da kasar Sin zata shigo dasu daga Amurka zai kai dalar Amurka biliyan 100. Na uku, idan Sin da Amurka suka yi hanzarin shawarwarin BIT wato yarjejeniyar zuba jari dake tsakaninsu, to adadin jarin da Amurka zata zuba a kasar Sin zai karu zuwa dala biliyan 50 a kowace shekara. Na hudu, idan sassan biyu sun karfafa hadin gwiwa bisa shawarar ziri daya da hanya daya, Amurka za ta samu babbar riba. Na biyar, idan sassan biyu su ingiza shawarwarin ciniki maras shinge, adadin cinikinsu zai karu cikin sauri. Don haka, a bayyane take ana iya fahimtar cewa, idan Amurka ta canja tunaninta, tabbas sassan biyu za su samu sakamako mai faranta rai.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China