180712-wasan-badminton-bello.m4a
|
Zuwa shekarar 1963, kungiyar wasan badminton ta kasar Indonesiya ta ziyarci kasar Sin. A lokacin kungiyar Indonesiya tana kan gaba a duniya, yayin da 'yan wasan kasar Sin ba su fara halartar gasannin kasa da kasa ba tukuna. Sai dai bayan da kungiyar Indonesiya ta yi wasanni da wasu kugiyoyi na kasar Sin, sakamakon wasannin sun ba mutanen duniya mamaki, ganin yadda 'yan wasan kasar Sin suka lashe abokan karawarsu na Indonesiya a dukkannin gasanin da suka gudana. Daga bisani, 'yan wasan kasar Sin sun fara taka rawa a gasanin kasa da kasa, tare da lashe lambobin zinariya da yawa. Zuwa yanzu, idan an duba jerin sunayen 'yan wasan badminton mafiya kwarewa a duniya, za a iya ganin sunayen 'yan wasan Sinawa maza da mata da yawa.
A nasu bangare, jama'ar kasar Sin suna son wasan badminton sosai. Ko a cikin CRI ma za a iya ganin ma'aikata da dama da suke zuwa aiki tare da jakar daukar kayayyakin wasan badminton, domin su halarci wasan bayan tashi daga aiki. Birnin nan da muke ciki, wato birnin Beijing yana arewacin kasar Sin. Watakila a sauran lardunan dake kudancin kasar, misali Fujiang da Guangdong, inda aka fara koyar da fasahar wasan badminton sosai, za a iya ganin karin jama'a da suke sha'awar wasan badminton.(Bello Wang)