in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron dandalin tattaunawa tsakanin kwararrun masana na kasar Sin da kasashen Afirka karo na bakwai
2018-07-05 15:10:06 cri



Daga ranar 4 zuwa 5 ga wata ne aka gudanar da taron dandalin tattaunawa tsakanin kwararrun masana na kasar Sin da kasashen Afirka karo na bakwai a nan birnin Beijing. Jakadun kasashen Afirka 44 da ke nan kasar Sin da jami'an gwamnati da shehunan malamai, da kuma wakilan kafofin yada labarai daga kasashen Afirka 52, da kuma jami'an da suka fito daga ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin da majalisar gudanarwa ta kasar da masanan kasar baki daya sama da 380 ne suka halarci taron.

A wajen bikin bude taron, Chen Xiaodong, mai taimakawa ministan harkokin waje na kasar Sin ya gabatar da Jawabi. A jawabin nasa ya ce, bana shekaru 40 ke nan da kasar Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, kuma a watan Satumba mai zuwa ne za a gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka. Shekarun 40 da suka shude sun kasance shekaru na ci gaban Sin da Kasashen duniya tare, haka kuma shekaru 40 ne da Sin da kasashen Afirka ke neman cigaba kafada da kafada.

Ya kuma yi watsi da zancen nan na wai "rancen kudin da kasar Sin ta samar wa kasashen Afirka ya tsananta matsalar basussuka da kasashen ke fuskanta.", A cewarsa, hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka na samar da nasarorin a zo a gani, wadanda kuma ke amfanawa al'ummar sassan biyu. Ya ce,"Idan muka waiwayi baya, za mu gane cewa, Sin da kasashen Afirka sun samu nasarorin a zo a gani a hulda da hadin gwiwa da ke tsakaninsu, wadanda kuma suka amfani al'ummar sassan biyu. Sai dai kullum akwai wasu mutanen kasashen yammacin duniya da ba su son ganin ci gaban hadin gwiwar Sin da Afirka, wadanda kuma ke neman cimma burinsu na musamman, suna ta shafa wa hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka kashin kaji, wadanda kuma a kwanan nan ne suka yi ta zargin cewa, wai "rancen kudin da kasar Sin ke samarwa kasashen Afirka ya tsananta matsalar basussuka da kasashen ke fuskanta", kuma "bisa ga kudaden jarin da take samarwa ne kasar Sin ke samu ikon kasashen Afirka sannu a hankali".

A ganin Chen Xiaodong, matsalar basussuka da wasu kasashen Afirka ke fuskanta ta samu ne daga dalilai da dama, wadanda kuma matsalar bai daya ce da kasashe masu tasowa kan fuskanta, kuma tabbatar da ci gaban kasa shi ne ainihin hanyar da za a bi wajen warware matsalar. Ya ce, "Mu kan ce koya wa mutane fasahar kamun kifi ya fi a ba su kifi kai tsaye. Alkawarin da muka dauka ne, haka kuma alkawarin da muka cika ne, inda muka taimaka wa kasashen Afirka samun kwarewar raya kansu."

A game da batun, Mr. Charles Onunaiju, daretan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin da ke Nijeriya ya bayyana cewa,"Lallai a gani na wannan kautar da tunani ne. Saboda a gaskiya ba wata kasa da za ta ci gaba, face tana da wani tsari na cin bashi, wannan shi ne tarihi na ci gaban ko da su kan su kasashen yamma. Kuma ko yanzu da muke maganan nan, Sin na da bashin da ya kai sama da dalar Amurka tiriliyan guda, na takardun bashin Amurka da take bi. Amma hakan bai mayar da Amurka wani yanki na Sin ba. Don haka ba abu ne mai yiwuwa, ka kai ga cimma cikakken ci gaba na zamani, daga dukkanin fannoni ba, face sai ka hada da karbar bashi daga ketare. Abun tambaya dai shi ne me ka yi da bashin? Samar da ababen more rayuwa, da shiga hada hadar dake iya samar da babbar riba, su ne hanyoyin da suka dace; a samar da makamashin lantarki, dukkanin su na cikin jigo na samar da cikakken tsarin ci gaba, a fannin ababen more rayuwa, kuma ba za su samu ba sai an yi rance. Kuma abun da nahiyar Afirka ke yi a fannin rance, wanda ke kunshe da bada lokacin cimma burin da aka sanya gaba, da karancin kudin ruwa, su ne hanyoyin rance mafiya dacewa, wadanda za su baiwa nahiyar damar bunkasa. Don haka duk wanda ke adawa da wannan, ba ya yiwa Afirka fatan samun ci gaba."

Bana shekaru 40 ke nan da kasar Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, kuma a watan Satumba da ke tafe za a bude taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka a birnin Beijing. A wajen taron na yini biyu, mahalarta taron sun tattauna bisa babban jigon nan na "huldar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka a yayin da Sin ke yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje." A game da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da Sin ta fara aiwatarwa yau da shekaru 40 da suka wuce, Mr.Onunaiju ya ce, "Zabin da Sinawa suka yiwa kan su, ya ba su damar fuskantar kalubalen dake gaban su. kamar yadda na bayyana, manufofin bude kofa ga waje, da gyare gyare a cikin gida, ba manufofi ne masu sauki ba. Shawara ce mai matukar tasiri, mai iya sauya komai. Wato za ta iya alamta makomar kasar ta fuskar ko za ta cimma nasara ko a'a. Ba a dauke ta da wasa ba. Ba shawara ce ta teburin shan shayi ba. Shawara ce mai matukar daraja da shugabannin kasar Sin suka aiwatar, bisa fahimtar su da ainihin yanayin kasar Sin, kuma suka maida hankali a kan ta; sakamakon hakan ne kuma muke gani a yau. Don haka ita ma Afirka, ya dace ta koma tushen ta, ta bincike ainihin halin da take ciki, ta gano matsalolinta, ta ina carbin ta ya tsinke? ta yi tunani mai zurfi domin gano hanyar bi mafi dacewa, ta kuma nacewa hanyar. Domin yanke kudurin hanyar da za a bi na da sauki, amma nacewa bin hanyar shi ne ke da matukar wahala, saboda irin kalubale, da wahalhalu da za a ci karo da su a hanyar."(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China