in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kauyen Liang-Jia-He(5)
2018-07-05 10:56:17 cri

A bakin kofar gidan da aka gina iri na kogon da aka haka a tsauni, an ga Wu Hui, mai shekarun haihuwa 14 wanda ke yin karatu a makarantar midil a kauyen Liang-Jia-He. A wancan lokaci, shekarun haihuwar Xi Jinping 15 ne kacal.

Saboda ana sanyi mai tsanani a cikin kogon, shi ya sa samarin da suka je kauyen daga birane domin samun horon aikin gona, suka tambayi Wu Hui cewa, ko yana iya kunna wuta domin dumama wurin saukarsu, Wu Hui ya ba da masa cewa, "Babu shakka zan iya."

Daga nan Wu Hui ya kan je wurin domin yin hira da samarin, sai dai samarin ba sa fahimci yaren gundumar Yanchuan, kuma shi ke yi musu bayani, Wu Hui ya yi farin ciki matuka yayin da yake sauraren hira da samarin suke yi, kana abun da ya fi jawo hankalinsa shi ne littattafan da samarin suka adana a cikin kogon.  

Littafi na farko da Wu Hui ya ara daga hannun Xi Jinping shi ne "Me ka sani game da duniyarmu", wanda ya bude wani sabon shafin kara fahimtar duniya gare shi. Daga baya sha'awarsa kan littafi ta karu cikin sauri, ya ci gaba da aron littattafai da dama daga wajen Xi Jinping, misali "Labari kan kasashe uku", da "Mahaifiya", da "Kogin Don mai shiru" da sauransu. Wu Hui ya koyi hallayar gaskiya da sahihanci daga Wang Yansheng da Lei Pingsheng. A sa'i daya kuma, ya koyi hallayar rashin nuna girman kai da son aiki fiye da magana daga Xi Jinping. Haka kuma a karkashin tasirin Xi Jinping, Wu Hui ya kara nuna sha'awa kan ilmi har ya tsai da kuduri cewa, zai yi kokarin shiga jami'a domin kara karatu a ciki.

A shekarar 1973, Wu Hui ya shiga jarrabawar shiga jami'a tare da Xi Jinping, kuma ya cimma burin shiga jami'ar horas da malaman makaranta ta Yan'an, kafin tashinsa zuwa jami'ar, Xi Jinping ya ba shi takardar sayen abinci kilo 15 kyauta, kana ya ba shi doguwar kwat mai launin shudi da Wang Yansheng bai tafi da ita ba, yayin tashinsa daga kauyen Liang-Jia-He. Xi Jinping shi ma ya gaya masa cewa, "Ka tafi da doguwar kwat, kana iya sa kayan a jami'a, kuma kana iya rufe jikinka da ita yayin barci."

Bayan da Wu Hui ya kammala karatunsa a jami'ar, ya taba yin aiki a ofishin nazarin aikin ba da ilmi na gundumar Yanchuan, da makarantar midil ta Yuju, da kwamitin kula da aikin ba da ilmi na garin Yongping, da makarantar midil ta Yongping da sauransu. Ko da yaushe ya kan yi kokari matuka, musamman ma a makarantar Yuju, wato bayan kokarin da ya yi, makarantar ta kai sahun gaba a cikin daukacin makarantun gundumar Yanchuan. Misali ya sa kaimi ga 'yan kasuwa da su zuba jari kan makarantar, domin kyautata sharadin makarantar. Ban da haka, har kullum Wu Hui kan tunatar da kansa a zuci da cewa, "Kada ka nuna girman kai, kada ka yi alfahari, a maimakon haka, ka mai da hankali kan hakikanin aikin da kake gudanarwa a yau da kullum."  

A shekarar 2014, Wu Hui ya yi ritaya, amma ya je makarantar domin yawo. Ba ya son barin makarantar, kamar yadda ake fada: "Ya kamata a yi rayuwa kamar haka: yayin da ya waiwayi rayuwarsa a baya, ba zai yi bakin ciki ba saboda ya himmantu kan aiki, kuma ba zai ji kunya ba saboda ya yi aiki mai ma'ana." Wu Hui yana ganin cewa, rayuwarsa tana da ma'ana.

Amma Xi Jinping fa, bisa dalilin iyalinsa, bai shiga jami'ar Tsinghua a shekarar 1973 ba.

Ya zuwa shekarar 1975, jami'ar Tsinghua za ta karbi dalibai guda biyu a gundumar Yanchuan, a don haka Xi Jinping ya sake shiga jarrabawar, abu mai faranta rai shi ne, kamfanin da mahaifinsa Xi Zhongxun ke aiki a birnin Luoyang na lardin Henan, shi ne ya samar masa da wata takardar shaida, inda aka bayyana cewa, "Kuskuren Xi Zhongxun ba shi da tsanani, ba zai kawo tasiri ga karatun 'ya'yansa ba."

A karshe dai, Xi Jinping ya shiga jami'ar Tsinghua.

Bisa kusantowar fara karatu a jami'ar, Xi Jinping yana ci gaba da aiki a kauyen, saboda bai zabi wanda zai maye gurbinsa na darektan karamar kungiyar 'yan jam'iyyar JKS a kauyen.

Shi Chunyang, wanda aka saba kiransa da sunan Suiwa yana da hali nagari, tun bayan da aka zabi Xi Jinping ya zama darektan karamar kungiyar 'yan jam'iyyar JKS a kauyen, sai Shi Chunyang ya zama mamba a karamar kungiyar. A bayyane take Xi Jinping yana ganin cewa, Shi Chunyang shi ne mafi dacewa, sai ya kira taron 'yan jam'iyyar JKS a kauyen, inda ya bayyana cewa, "Zan bar nan, dole kuma mu zabi sabon darektan kungiyarmu, ina ganin cewa, Suiwa ya fi dacewa." Daga nan sai daukacin 'yan jam'iyyar suka zabi Suiwa ya zama darektan karamar kungiyar 'yan jam'iyyar JKS a kauyen Liang-Jia-He. Game da wannan, Shi Chunyang ya ce, "Na san dalilin da ya sa haka, hakika ba domin na fi rinjaye ba ne, a'a kawai domin manoman kauyenmu sun nuna amincewa ga Xi Jinping, suka zabe ni bisa shawararsa."

Shi Chunyang ya gaya mana wani batun da ba zai manta ba har abada.

Ba da dadewa ba bayan da aka zabi Xi Jinping a matsayin darektan karamar kungiyar 'yan jam'iyyar JKS a kauyen, sai an bai wa kauyen wasu abinci a matsayin ceto, amma manoman kauyen ba su cimma matsaya daya ba kan yadda za su raba abincin. Sai Xi Jinping ya gabatar da shawara cewa, "Ya fi dacewa mu je gidajenku mu duba wa ya fi bukatar abincin, ko hakan zai yi ko a'a?"

Daga yammacin karfe 10 har zuwa karfe 5 da asuba, Xi Jinping ya je ko wanen gidajen kauyen tare da sauran manoma daya bayan daya, a karshe dai sun gano wa ya fi bukatar taimakon, da haka aka rarraba abincin lami lafiya, ba wanda ya nuna kiyayya.

Shi Chunyang ya ce, lamarin ya burge shi matuka, yana mai cewa, "Hanyar gudanar da aiki ta Xi Jinping tana da inganci, shi ya sa ta samu sakamako mai gamsarwa. Lallai idan wani mutum ba shi da tunanin son kai, zai iya gudanar da aiki bisa adalci, jama'a kuwa za su nuna masa amincewa, kana hanyar gudanar da aiki ita ma tana da muhimmanci matuka, dole ta samu karbuwa daga saura."

Xi Jinping ya tashi daga kauyen Liang-Jia-He ne a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 1975, lokacin da ya bude kofar kogonsa da safiyar wannan rana, ya ga mutane da yawa suna tsaye shiru ko ina, daukacin manoman kauyen sun zo yin ban kwana da shi, tare da tsaraba, nan take hawaye suka zubo daga idanun Xi Jinping.

Wannan rana manoman kauyen ba su je aiki a gonaki ba, dukkansu sun zo sun tsaya nan a layi domin yin ban kwana da Xi Jinping, har suka raka shi nisan kilomita sama da biyar.

Bayan shekaru da dama da suka gabata, Xi Jinping ya waiwayi rayuwarsa a kauyen Liang-Jia-he, yana mai ganin cewa, kauyen yana da ma'ana ta musamman gare shi, yana mai cewa, "Na tsaya kan kasa tare da al'ummun kasa, hakan ya karfafa mini zuciya, tudun dake arewacin lardin Shaanxi gari na ne, inda na samu imanin bautawa al'ummar kasa, duk da cewa na bar wurin, amma na adana zuciyata a wurin."

Tun daga lokacin da Xi Jinping ya tashi daga kauyen Liang-Jia-He, Shi Chunyang bai taba daina yin tunanin gudanar da aiki bisa adalci ba.

Sannu a hankali Shi Chunyang ya tarar da cewa, a zamanin da ake fama da matsalar karancin kayayyaki, gudanar da aiki bisa adalci ya fi muhimmanci, amma yanzu wato a zamanin da ake samun saurin ci gaban tattalin arziki, abu mafi muhimmanci shi ne wadata, to ta yaya za a iya cimma wannan buri? Shi Chunyang ya gabatar da shirin raya tattalin arzikin gundumar Yanchuan ta hanyar shuka itatuwan tofa, bisa hakikanin yanayin da gundumar ke ciki.  

A ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 2015, Xi Jinping ya komo kauyen Liang-Jia-He don ganawa da manoman kauyen. Da ya ji an ce an shuka itatuwan tofa a kan tudun, sai ya ce yana son ya je duba itatuwan, darektan karamar kungiyar 'yan jam'iyyar JKS a kauyen Shi Chunyang ya yi masa bayani cewa, "Ana bukatar kudin RMB yuan dubu daya kan gonar shuka itacen tofa mai fadin hekta 0.07. Itacen zai samar da tofa bayan shekaru biyar, kana a ko wace shekara ana iya samun kudin shiga yuan sama da dubu daya zuwa dubu 20 daga itatuwan."

Da Xi Jinping ya ji bayanin Shi Chunyang, ya kuma yi farin ciki, ya yi dariya, ya bayyana cewa, ashe Suiwa ya kware wajen kara yawan kudin shigar manoman.

Tun daga shekarar 2014, masu yawon shakatawa da suke zuwa kauyen Liang-Jia-He bude ido sun karu, a don haka kauyen ya kara mai da hankali kan aikin yawon shakatawa, har aka kai ga kafa kamfanin raya yawon shakatawar al'adun kauyuka a kauyen a ranar 1 ga watan Mayun shekarar 2015. Darektan karamar kungiyar 'yan jam'iyyar JKS a kauyen Shi Chunyang ya gayyaci masanan da abin ya shafa, da su tsara tsarin gudanar da harkokin kamfanin, manoman kauyen, su kasance ma'aikatan kamfanin, wato kusan kaso 60 bisa dari na manoman kauyen suna aiki ne a gaban kofar gidajensu.

An rika samun ci gaba sannu a hankali, labari game da "gudanar da aiki bisa adalci" shi ma bai tsaya nan ba, saboda ci gaban zamani ba shi da iyaka, labarin gudanar da aiki bisa adalci shi ma ba shi da karshe.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China