Shugaban tawagar jakadun Sin dake Turai Mista Zhang Ming ya bayyana a jiya 2 ga wata a Brussels cewa, ganawa karo na 20 tsakanin shugabannin Sin da Turai, wadda za a gudanar a birnin Beijing, za ta ba da jagoranci a siyasance, wajen kara bunkasa dangantakar Sin da Turai cikin dogon lokaci, kuma hadin gwiwar Sin da Turai mai karko zai zama mataki da zai ba da gudunmawa mai yakini ga duniya, wadda ke fuskantar sauye-sauye da takara sosai.
Mista Zhang ya yi wannan batu ne, yayin da ya halarci taron hangen nesa, gabanin ganawar shugabannin Sin da Turai, da kungiyar abokan Turai ta gudana a wannan rana. (Amina Xu)