in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron karawa juna sani game da fasahar noman ciyayi da laimar kwadi
2018-07-12 17:14:06 cri

A kwanakin baya ne aka shirya taron karawa juna sani na kasa da kasa karo na 16 game da fasahar noman ciyayi da laimar kwadi a birnin Fuzhou na lardin Fujian dake nan kasar Sin.

Manufar taron ita ce, amfani da wannan fasaha wajen kare zaizayar kasa da matsalar kwararar Hamada baya ga yadda al'umma za ta ci gajiyar laimar kwadi a matsayin abinci da kuma fannin magunguna.

Bincike da masana kasar Sin da suka fara gano fasahar suka yi, ta nuna cewa, ana amfani da laimar kwadin wajen maganin hawan jini da shanyewar jiki, da kuma kara karfin garkuwar jiki.

Yanzu haka akwai kasashen Asiya da na Afirka da suka hada da Papau New Guinea da Afirka ta kudu da Najeriya da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da sauransu.

Bugu da kari, yayin taron wakilai daga sassa daban-daban sun bayyana yadda gwamnatocin kasashensu ke daukar matakan kara cin gajiyar wannan fasaha. Baya ga ma'aikatansu da yanzu haka ke kara samun horo a nan kasar Sin.

Masu fashin baki na cewa, wannan fasaha za ta taimaka wajen magance matsalar rikicin manoma da makiyaya baya ga samar da magunguna da abinci mai gina jiki da kuma uwa uba aikin yi ga mata da matasa.

Haka kuma fasahar ta kara kyautata alakar Sin dake kasashen Afirka a fannin noma, fasahohi da musayar jami'ai da guraben karo ilimi da kasar Sin ke baiwa daliban kasashen nahiyar. (Saminu, Ibrahim/ Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China