A jawabin da ya gabatar, wakilin dindindin na kasar Sin a dake MDD, jakada Ma Zhaoxu ya ce kasarsa na goyon-bayan kasa da kasa su kara karfin murkushe ayyukan ta'addanci.
Ma Zhaoxu ya ce, ta'addanci wani babban makiyin bil'adama ne. A don haka ya zama dole kasashen duniya su zama tsintsiya madaurinki daya wajen raya makoma ta bai daya ga daukacin bil'adama. A yayin taron, Ma ya gabatar da wasu muhimman shawarwarin kasar Sin kan yadda za'a yi don kara karfin murkushe ayyukan ta'addanci, ciki har da cimma matsaya daya a fannin yaki da ta'addancin, da daukar matakai daga dukkan fannoni, da karfafa hadin-gwiwa tsakanin kasashe daban-daban, da aiwatar da yarjeniyoyin da abun ya shafa da sauransu.
Ma ya kuma alkawarta cewa, kasarsa za ta ci gaba da samar da tallafi ga kasashe masu tasowa a fannin yaki da ta'addanci, da hada kai kafada da kafada da sauran kasashen duniya, domin wanzar da zaman lafiya a fadin duniya.(Murtala Zhang)