Yang Jiechi ya ce, bana shekara ce ta cika shekaru 20 da kulla dangantakar diflomasiyya tsakanin Sin da Afirka ta Kudu. Ana saran Shugaba Xi Jinping zai je Afirka ta Kudu a watan Yuli don halartar taron shugabannin kasashen BRICS karo na 10, sa'annan a watan Satumban bana, shugaba Xi da takwaransa na Afirka ta Kudun, Cyril Ramaphosa za su shugabanci taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar Sin da Afirka wato FOCAC. Kasar Sin na fatan karfafa hadin-gwiwa da mu'amala da Afirka ta Kudu, don cimma nasarar shirya wadannan ayyuka biyu, da kokarin habaka huldar kasashen biyu.
A nata bangaren, Duba ta ce, kasarta za ta yi kokarin inganta hadin-gwiwa tsakanin kasashen BRICS da Afirka gami da kasar Sin.(Murtala Zhang)