in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya Kamata Gwamnatocin Arewacin Najeriya Su Rika Samar da Filayen Wasanni A Cikin Al'umma -Dan Isan Dutse
2018-06-28 13:38:20 cri
Wani labari da shafin Intanat na Leadershipayau ya wallafa na cewa, An yi kira ga Gwamnatocin jihohin Arewacin Najeriya da su rika samar da filayen wasanni saboda yanzu akwai unguwanni sababbi, amma abin takaici sai ka ga babu filayen wasanni. Hakimin Chamo. Dan isan Dutse. Alhaji Zahradden Sunusi shi ne ya bayyana haka, lokacin da ya wakilci mai martaba sarkin Dutse a wajen gasar tseren ninkayar ruwa na yara da a ka yi a kano. Yayi nuni da cewa, rashin irin wadannan filayen wasanni suna sabbaba wasu matasa tunane-tunane har ma su fada harkar shaye-shaye. Hakimin na Chamo ya ce yana da kyau bayan an samar da filayen wasanni a rika samar da kayayyakin wasannin da matasa za su rika koyon wasanni iri-iri domin harkar wasa baya ga motsa jiki da nishadi ta zama babbar sana'a a duniya. Dan Isan na Dutse ya ce yana da kyau majalisun dokoki da ake da su tun daga mataki na kansiloli, da na jaha da na kasa wakilai da sanatoci su samar da dokoki masu karfi na hana mutane mallake filayen wasanni, saboda yana faruwa filaye da aka ware dan wasanni sai a dauka a ba wasu, hana irin wannan zai sa a yi wa al'umma gata a dadada musu a samu ci gaba. Alhaji Zahradden Sunusi ya ce,su dama a masarautar Dutse suna ba harkar wasanni goyon baya, yanzu haka ma za a soma wasan kwallon gwaf "Golf" a jahar jigawa inda 'yan wasa daga sassan kasar nan za su halarta wanda hakan zai tallafa wajen habaka tattalin arzikin jahar ta saukar baki da saye da sayarwa da ma saka hannun jari ga masu sha'awar kafa kasuwanci a jihar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China