180628-gani-da-ido-luba.m4a
|
Bana ake cika shekaru 55 da kafuwar sashen Hausa na CRI. A cikin shekarun nan 55, sashen Hausa ya yi ta kokarin samar da shirye-shirye masu ilmantarwa, da nishadantarwa ga masu sauraronsa da ke fadin kasashen yammacin Afirka. Ya kuma kulla alaka da zumunta da masu sauraronsa da yauwa. A yau za mu ba ku labarin wani bawan Allah daga cikinsu, wanda a yanzu haka yake birnin Tianjin da ke arewacin kasar Sin, wanda ma iya cewa a sabo da sauraron sashen Hausa na CRI ne ya kulla alaka ta musamman da kasar Sin, har ma a cewarsa hakan ya kawo sauyi ga rayuwarsa. A kwanan baya, wakiliyarmu Lubabatu ta hadu da shi a birnin na Tianjin, ta kuma samu damar tattaunawa da shi.
Yanzu sai a gyara sautin rediyo, a saurari wannan hira, don samun karin haske dangane da labarinsa. (Lubabatu)