in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CRI Hausa ya samu lambar yabo ta ASAUNIL ta jamhuriyar Nijar
2018-06-27 14:56:54 cri

Kungiyar Marubuta ta kasa ASAUNIL ta karrama sashen Hausa na gidan Rediyon Kasar Sin CRI da lambar yabo bisa kokarin da yake wajen bunkasa harsunan Afrika musammun ma harshen Hausa a Nijar tare da gidajen rediyo na kasashen waje wato BBC, VOA, DW, RFI da kuma REDIYO IRAN dake watsa shirye shiryensu cikin harshen hausa a jamhuriyyar Nijar domin cigaban zaman takakewar al umma, tattalin arziki, ilimi, muhalli, zaman lafiya da dai sauransu, Ita dai kungiyar ASAUNIL, kungiya ce dake kokarin kiyaye da bunkasa harsunan kasar Nijar. Bikin mika wadannan lambobin yabo ga wadannan gidajen rediyo ya gudana ne a ranar Asabar a zauren shawara na Palais Des Congres dake birnin Yamai, hedkwatar kasar Nijar a lokaci guda tare da bikin mika tukwici ga marubutan da suka lashe gasar rubutu da harsunan gida karo na farko da aka yi ma taken Tukwicin Forfesa Mahamadu Hambali Junju a karkashin jagorancin ministan yada al'adu Asumana Malan Isa da kuma shugaban kungiyar ASAUNIL malam Abduwa Mainasara tare da sauran manyan baki da suka fito daga yankunan kasar mu da ma kuma tarayyar Najeriya. Wakilin sashen hausa na CRI, Mamane Ada ya karbi wannan kyauta da sunan CRI HAUSA.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China