Manzon na Sin wanda ya bayyana hakan yayin zaman muhawarar kwamitin sulhun MDD game da kasar ta Afghanistan, ya ce kamata ya yi kungiyar Talibin ta shiga a dama ta ita a shirin wanzar da zaman lafiyar da gwamnatin Afghanistan ta bullo da shi, kana ta ba da gudummawar ganin an samar da zaman lafiya a kasar.
Ya ce, sasantawa, ita ce hanya mafi dacewa ta warware batun kasar. Kasar Sin a nata bangare tana goyon bayan shirin da gwmnati da al'ummar kasar suka amince da shi na samar da zaman lafiya da sasantatawa.
Jami'in na Sin ya ce a matsayinta na dadaddiyar kawa dake makwabtaka da Afghanistan, kasar Sin tana fatan ganin an samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaro da ma ci gaba cikin sauri a kasar. (Ibrahim)