in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD: Afghanistan na cikin hali mai kyau a siyasance
2018-06-27 13:36:25 cri

A jiya ne wakilin musamman na MDD mai kula da harkokin Afghanistan Tadamichi Yamamoto ya sanarwa kwamitin sulhu na MDD cewa, shirin mika mulki na kasar na tafiya yadda ya kamata, sai dai ya bayyana damuwa game da sauran batutuwa, duk da cewa gwamnatin hadin kan kasar ta bayyana niyyar yin shawarwari ba tare da gindaya wasu sharuda ba a yayin taron da ya gudana a Kabul a watan Fabrairu, a kokarin da ake na samar da wani sabon yanayi mai kyau na tabbatar da zaman lafiyar a kasar.

'Yan kasar dai na fatan samun zaman lafiya, yayin da shi ma shugaban kasar Ashraf Ghani ya dauki kwararan matakai na ganin an shimfida zaman lafiya ta hanyar yin shawarwari.

Tadamichi Yamamoto ya ce, za a yi zaben majalisar dokokin kasar a watan Oktoba na bana sa'an nan a shirin gudanar da babban zabe a lokacin bazarar badi.

Tadamichi Yamamoto ya kara da cewa, gwamnatin Afghanistan ta tsagaita bude wuta a lokacin bikin karamar sallah, kuma tana kokarin tsawaita wannan wa'adi, amma kungiyar Taliban ta fara kai hare-hare, abin da ya haifar da bacin rai sosai. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China