in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya bada umarnin yaki da miyagun kwayoyi
2018-06-25 16:12:15 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bada umarnin aikin yaki da miyagun kwayoyi, inda ya jaddada cewa, ya kamata a kara jagorancin jam'iyya da yin amfani da rinjayen kasa a fannin siyasa da manufofi, da kuma kyautata tsarin yaki da miyagun kwayoyi, da tabbatar da sauke nauyin dake wuyan kowane daidaikun jama'a, da kara kwarin gwiwar jama'a wajen yaki da miyagun kwayoyi, don bin wata hanya ta musamman na kasar Sin wajen yaki da miyagun kwayoyi ta yadda za a cimma nasara a sabon karni.

Xi Jinping ya nuna cewa, wannan aiki yana da alaka sosai wajen tabbatar da tsaron kasar, da bunkasuwar al'umma, da kawo moriyar jama'a, ya kamata a maida hankali kan wannan aiki har a tabbatar da kawar da shi baki daya. Xi Jinping ya ce, kamata ya yi, a gudanar da aikin yaki da miyagun kwayoyi bisa doka, da kara karfi a wasu muhimman yankuna, da kyautata tsarin yaki da shi, da kawar da tushensa baki daya, da kuma kara horar da matasa a wannan fanni.

An bada labari cewa, a watan Disambar shekarar 1987, a babban taron MDD karo na 42 an zartas da kudurin sanya ranar 26 ga watan Yuni a matsayin ranar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa. Ranar yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa na wannan shekara na kasar Sin na da taken "Kawar da miyagun kwayoyi don yin zaman rayuwa lami lafiya." (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China