in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya ya yabawa kungiyar Super Eagles bisa doke Iceland da ta yi
2018-06-23 16:24:40 cri
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yabawa kungiyar kwallon kafa ta kasar wato Super Eagles, bayan da ta doke Iceland a rukuni na D a wasan cin kofin duniya dake gudana a Rasha.

Cikin wata sanarwa, Muhammadu Buhari, ya ce yakini da da'a da hadin kai da jajircewa da matasan na Nijeriya suka nuna ne ya kai sa ga samun nasara.

Dan wasan gaba na Super Eagles Ahmad Musa, shi ne zakaran da ya ci wa kasar kwallaye biyu da ta kai ta ga lallasa Iceland da ci 2 da nema, a wasan da suka buga jiya da yamma a filin wasa na Volgograd.

Shugaba Buhari ya jinjinawa 'yan wasan kungiyar bisa kokarin da suka yi, inda ya kuma bukaci su ci gaba da wannan kuzari har ya kai su ga doke Argentina a wasan karshe da za su buga a rukunin na D.

Muhammadu Buhari ya ce yana da yakinin cewa 'yan wasan sun yi imanin za su samu cancantar fita daga rukunin na su mai wuya har ma su yi nisa a gasar.

Nasarar ta sanya 'yan Afrikan zama na biyu a rukunin D, inda suke bayan Croatia, abun dake nufin cewa su na da gagarumar dama idan suka kauracewa shan kayi a hannun Argentina a wasan karshe na rukunin, duk da cewa nasara ga Argentina zai ba bangaren kudancin Amurka damar shiga zagaye na gaba. Sannan Iceland na da kankanuwar dama ta samun cancanta idan ta doke Croatia. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China